Messi da Ronaldo za su fuskanci juna a Saudi Arabia

An wallafa

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo na shirin fuskantar juna, bayan da Inter Miami za ta kara da Al-Nassr a wasan sada zumunta a Saudi Arabia cikin watan Fabrairu.

Haka kuma a wasan za a lashe kofi na Riyadh, don shirin tunkarar kakar badi, inda Inter Miami za kuma ta kece raini da Al-Hilal ranar 29 ga watan Janairu.

Tun farko Maimi ta yi watsi da batun cewar za ta shiga wasannin a Saudi Arabia a lokacin da aka fara batun a cikin watan Nuwamba.

Messi da Ronaldo, wadanda ake cewa ba kamarsu a fannin taka leda a duniya, sun fara fuskantar juna a tamaula a 2008, lokacin da Barcelona ta doke Manchester United a Champions League karawar daf da karshe.

Jimilla sun fuskanci juna sau 34, inda kyaftin din Argentina ya yi nasara 16, Ronaldo da 10 suka yi canjarras tara.

Cikin haduwa 35 da suka yi, Messi ya ci kwallo 21 ya bayar da 12 aka zura a raga, shi kuwa Ronaldo 20 ya ci ya kuma bayar da daya aka zura a raga.

Inter Miami ta kammala gasar kwallon Amurka a mataki na 14 a bara, sun lashe Leagues Cup tare da Messi, wanda ya koma kungiyar a watan Yuli da cin kwallo 10, wanda hakan ya sa ta lashe kofin farko a tarihi.

Saudi Arabia na kashe makudan kudi wajen bunkasa kwallon kasae, wadda take sayan fitattun 'yan wasa ciki har da Ronaldo da Karim Benzema da Sadio Mane da N'Golo Kante da Jordan Henderson da sauransu.