Yadda kungiyar IS ke yunkurin maido da daularta a Afirka

Asalin hoton, IS
Kungiyar IS na kira ga mambobinta da su yi hijira zuwa Afirka, inda take kokarin sake gina shelkwatarta wadda a baya aka sani a Gabas ta Tsakiya.
A watan Yuni kungiyar ta fito karara ta bayyana aniyar daukar sabbin mambobi a Afirka, a daidai lokacin da daulolinta a Iraki da Siriya ke cika shekara takwas da kafuwa.
Sannu a hankali kungiyar na kara karfi a nahiyar Afirka tun shekarar 2019 - lokacin da aka daina jin duriyarta a yankin Gabas ta Tsakiya - inda a yanzu rassan kungiyar a Afirka ke zama masu karfi ta fannin kai hare-hare.
Alal misali, yadda kungiyar take gudanar da ayyukanta a Najeriya 'yar manuniya ce game da yadda take samun karfi a kasar, duba da yadda take kara zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan, har zuwa wuraren da a baya ba a saba ganin tana kai su ba.
A ranar 6 ga watan Yuli ne kungiyar ta kai wani mummunan hari gidan yarin Kuje da ke Abuja babbab birnin kasar, inda ta kubutar da mambobinta sama da 60.
Kawo yanzu kungiyar na da manyan rassa a Afirka da suka hadar da:
ISWAP ta Yammacin Afirka da ke ayyukanta a Najeriya da Chadi, da Kamaru, da wasu yankunan Jamhuriyar Nijar.
Sai kuma ISACP ta Tsakiyar Afirka da ke ayyukanta a kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, da Uganda, da kuma Mozambique
Da kuma rassan kungiyar na yankin Sahel da ke ayyukansu a Mali da Somaliya.
Sakonni: 'Afirka, kasar hijira da jihadi'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A baya-bayan nan kungiyar ta saki wani faifan bidiyo na farfaganda tare da wasu sakonni biyu a wata jaridarta mai suna al-Naba, wanda a cikin sakonnin kungiyar ke kira ga mambobinta da su yi hijira zuwa Afirka.
Sako na farko da ta fitar ranar 10 ga watan Yuni, na yin shagube ga dakarun kawancen da ke yaki da kungiyar a Afirka. ''Cewa kungiyar za ta fadada ayyukanta domin kafa Daula a Afirka''.
Sakon wanda ke dauke da taken 'Wanzuwa da fadadar ISIS a Afirka''. Na nuna cewa za ta kara daukar mambobi domin fadada ayyukanta a nahiyar ta afirka.
Musamman saboda janyewar sojojin farsana a Mali da kuma mayar da hankali da kasashen yamma suka yi kan yakin Ukrainne.
Kwana hudu bayan sakon na farko sai kungiyar ta saki wani faifan bidiyo na farfaganda, wanda a ciki a ka ga yadda mayakan kungiyar ke gudanar da ayyukansu.
Da suka shafi addini da sauran al'amura, wadanda kuniyar ta ce a Borno da ke arewa maso gabashin ajeriya aka dauki bidiyon.

Asalin hoton, IS
Abinda da bidiyon ke nunawa shi ne cewa yanzu kungiyar ce ke iko da wasu yankuna a Afirka ta yamma, abin da kuma zai iya ba ta damar daukar sabbin mambobi a ko'ina a fadin duniya.
A cikin bidiyon wanda ake magana da harshe Hausa tare da tsarma harshen Larabci a wasu lokatan an yi kokarin sauya tunanin mutane game da yadda suke kallon kugiyar a matsayin mai hadari, tare da kokarin nuna musu cewa kungiyar garkuwa ce a gare su.
Wannan kuma shi ne salon da suka fara amfani da shi a birnin Mosul na Irakia farkon shekarar 2014 bayan da ta ayyana daularta a kasar.
Kwana biyu bayan sakin wannan bidiyon kungiyar ta sake yunkurowa domin wallafa wani sakon a jaridarta ta al-Naba. da aka yi wa take da ''Afirka kasar hijira da jihadi'' wanda ke kokarin tabbatar da sakon da bidiyon ke dauke da shi.
Jaridar ta yi kokarin kamanta karfin kungiyar a Afirka da kuma yadda take a farkon kafuwarta yankin gabas-ta-tsakiya.are kuma da yin kira ga al'umma da su yi hijira zuwa Afirka domin rabauta da jihadi.
Kungiyar ta kara samun kwarin gwiwa ne a Afirka a watan Mayun shakarar da ta gabata.
bayan da ta yi nasarar karya karfin kungiyar Boko Haram ta hanyar kashe shugabanta Abubakar Shekau tare kuma da kame sansanoninta da daukar wasu daga cikin mayakan Boko Haram.

Asalin hoton, Islamic State Propaganda
Yunkurin kugiyar na maido da ayyukanta Afirka, ya faro ne tun tsakiyar shekarar 2019, bayan da ta rasa iko da yankin Baghouz a gabashin Siriya.
wanda shi ne waje na karshe da ta rasa a daulolinta da ke gabas-ta-tsakiya.
A lokacin ne kungiyar ta ayyana kafuwar rashenta a yankin Sahel a kasashen DR Kongo da Mozambique.
Kari a kan wadanda dama tuni take da su wato (ISWAP) da kuma ta Somaliya a yakin Afirka.
A wata shidan farko na shakarar 2022 kungiyar ta dauki alhakin hare-hare a
Najeriya ce kasar da kungiyar ta fi kai hare-hare inda ta kai guda 282, DR Kongo mai 86 da Mozambique mai 57.
A watan Yuni kungiyar ta kara kaimi wajen kai hare-hare fiye da watannin da suka gabata.
A watan da ya gabata IS ta dauki alhakin hari 173 a afadin duniya, wadanda kuma guda 100 daga cikinsu ta kai su ne a Afirka.
Rassan da suka fi kai hare-hare su ne ISWAP da ke da shelkwata a Najeiya mai 44, sai ISCAP mai shelkwata a DR Kongo da ta kai hari 23 a DR Kongo da 33 a Mozambique.

Asalin hoton, Islamic State Propaganda
Mozambique ce kasar Afirka da hare-haren ISIS suka fi shafa a watan na Yuni, inda suka rika kai hari kan kauyuka da kuma arewacin kasar inda a baya ba ta fiye kai hari ba.
Haka kuma a wannan shekarar ISIS ta kara zafafa hare-hare kan wasu kingiyoyin ta'addaci a Mali.
Inda kungiyar ta yi ikirarin kai muggan hare-haren da suka yi sanadiyar karbe iko da wasu yankuna da a baya ke hannun kungiyoyin, al-Qaeda, da Tuareg.
Tare da fatan samun karin karfi bayan ficewar dakarun Faransa daga Ma a 'yan watanni masu zuwa.
Kawo yanzu dai Kasar Somiya ce kawai ke yi wa kafuwar ISIS tutsu.
Wannan ko baya rasa nasaba da yadda kungiyar al-Shabab mai samun goyon bayan al-Qaeda ke da gagarumin karfi a kasar.
A halin da ake ciki kungiyar ta fi fitar da bidiyon ayyukanta daga nahiyar Afirka da ke dauke da hotuna da faya-fayan bidiyoyin da ke nuna irin barnar da hare-harenta suka yi.
'Fadadar ISIS'
Ta hanyar sakonnin da ta saka a baya-bayan nan kungiyar ta yi ikirarin kara fadada yankuna dake hannunta tare manufofin kungiyar a nahiyar Afirka.
Za a iya tabbatar da hakan idan aka yi la'akari da wuraren da ta kai wa hari a wannan shakarar, wadanda a baya ba ta taba kai musu hari ba.
A Najeriya alal misali, tun watan Afrilu kungiyar ke daukar alhakin hare-hare a tsakiya tare da kudancin kasar, wuraren da baya ba ta saba kai musu hari ba.
A wannan shekarar ISIS ta fara daukar alhakin kai hari a jihohin Kogi, da Taraba, da Kaduna, da kuma jihar Naija.
A ranar 5 ga watan Yuli kungiyar ta kai harin farko a kan gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin kasar, harin da ta yi ikirarin cewa gagarumar nasara ce a gareta.

Asalin hoton, IS
Sabbin rassan kungiyar
A watan Yuni ISIS ta fara daukar alhakin hare-hare a sababbin wurare a arewacin kasar Mozambique.
A watan da ya gabata kungiyar ta dauki alhakin hari na farko a kudancin kasar a yankin Cabo Delgado wanda ke gundumar Ancuabe .
Akwai wani harin kuma kuma da ta kai wa masana'antar hakar ma'adinar mallakar kasar Australia a gundumar ta Ancuabe.
A karon farko da wata masana'antar kasar waje rufe ayyukanta a kasar saboda matsalar tsaro.
Haka kuma a wannan watan dai kungiyar ta kai harin farko a yankin Nampula na kasar.
Abinda kuma ya sanya kungiyar ikirarin fadada ayyukanta a kasar Mozambique

Asalin hoton, Islamic State
A watanni shidan farko na wannan shekara ISIS ta yi ikirarin kwace iko da wasu karin yanku biyu, daya a yankin Sahel da kuma daya a Mozambique.
Ana ganin reshen na Mozambique zai hade da babban reshen kungiyar da ke tsakaiyar Afirka na (ISCAP) wanda ke gudanar da ayyukansa a DR Kongo, da Uganda, da wasu yankuna na Tanzaniya.
Saboda tun shekarar 2019 kungiyar ke daukar alhakin hare-hare a Mozambique karkashin reshen ISCAP
Sabon reshen kungiya na yankin Sahel dake kasar Mali- da aka kafa a watan Maris na aiki ne kafada-da-kafada da takwaransa na ISWAP da ke Najeriya.
Kuma tun watan Maris din shekarar 2019 reshen ke daukar alhakin hare-hare a yankin Sahel.
wadannan sauye-sauye da kungiyar ke samu ta fuskar wuraren da take iko da su tare da sabbin shugabanni.
Za su taimaka wa kungiyar matuka wajen fadada ayyukanta a nahiyar Afirka.
Ana tunanin wadannan sauye-sauye wani shiri ne da sabon shugaban kungiyar na duniya Abu al-Hasan al-Hashimi al-Qurashi, ke yi domin karfafa shugabancinsa.
A yanzu dai wadannan rassa na kara samun karfi gwiwwa bayan ayyana su a matsayin rassan ISIS da uwar kungiyar ta duniya ta yi.











