'Yan Real Madrid da suka je Espanyol buga La Liga

Benzema and Hazard

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Espanyol, domin buga wasan mako na uku a gasar La Liga da za su kara a RCDE Stadium ranar Lahadi.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara a La Liga, inda ranar 3 ga watan Oktoba Espanyol ta ci Real Madrid 2-1.

A wasa na biyu kuwa Real ta yi nasara a gida da cin 4-0 ranar 30 ga watan Afirilun 2022.

Kawo yanzu Real Madrid mai rike da La Liga tana da maki shida a wasa biyu, bayan da ta doke Almeria 2-1 da cin Celta Vigo 4-1.

Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan kwallon da ya je da su Espanyol.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Rüdiger da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni da kuma D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.

Benzema da Ancelotti sun lashe kyautar bajinta a gasar kungiyoyin Turai

Karim Benzema da Carlo Ancelotti suna daga cikin wadanda suka lashe babbar kyautar karramawa da UEFA ta gudanar a Istanbul Turkiya ranar 25 ga watan Agusta.

Benzema and Ancelotti

Asalin hoton, Real Madrid

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bajintar da Karim Benzema ya yi

Benzema shi ne ya lashe kyautar dan kwallon da ba kamarsa a kakar 2021/22.

Kyaftin din Real Madrid ya samu yawan kuri'u masu yawa, yayin da Courtois ya yi na biyu da Kevin de Bruyne a mataki na uku.

Dan kwallon tawagar Faransa ya taka rawar da Real ta lashe Champions League na 14 da La Liga da kuma Spanish Super Cup da cin kwallo 44 a kakar da ta wuce.

Haka kuma shi ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a zura kwallaye a raga a Champions League mai 15.

Bajintar da Carlo Ancelotti ya yi

Carlo Ancelotti shi ne ya lashe kyautar mai horar da tamaula da ba kamarsa a kakar da ta gabata, bayan daukar Champions League da La Liga da kuma Spanish Super Cup.

Kociyan ya haura Jurgen Klopp na Liverpool da kuma na Manchester City, Pep Guardiola da ywan maki.

Dan kasar Italiya ya zama na farko da ya lashe Champions League hudu, kuma shi ne na daya da ya dauki kofin lik a manyan gasar Turai biyar, wato Sifaniya da Jamus da Faransa da Ingila da kuma Italiya.

An raba jadawalin Champions League

 

 

Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Alhamis aka raba jadawalin Gasar Zakarun Turai kakar 2022/23.

Real Madrid ce ke rike da kofin kuma na 14 jumulla, an hada ta rukuni na shida da ya hada da RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic

Za a fara wasannin cikin rukuni ranar Talata 6 ga watan Satumbar 2022

                Borussia Dortmund da FC Kobenhavn

                GNK Dinamo Zagreb da Chelsea

                Sevilla da Manchester City

                Paris Saint-Germain da Juventus

                Celtic Glasgow da Real Madrid

                SL Benfica da Maccabi Haifa         

                Red Bull Salzburg da AC Milan        

                RB Leipzig da Shakhtar Donetsk