McCarthy ya zama sabon shugaban majalisar Amurka

An wallafa

Dan majalisar wakilan Amurka karkashin jam'iyyar Republican, Kevin McCarthy ya zama sabon shugaban majalisar kasar.

Hakan ya biyo bayan samun rinjaye a kuri'un da aka jefa bayan karo 15 ana kai ruwa rana tsakanin shi da wasu jam'iyyarsa da ke adawa da shi.

An shafe kwanaki hudu, da kuma jefa kuri'a sau 15, ba tare da ya samu adadin kuri'u 217 ba da yake nema ya dare kujerar.

Mai bi masa Hakeem Jeffries na Democrats ya samu 212.

Mista MacCarthy ya samu goyon bayan tsohon Shugaba Donald Trump, sai dai hakan bai hana ya samu masu adawa da shi ba, wadanda da kyar ya shawo kansu suka zabe shi.

Ko a 1860 an taba samun irin haka, inda aka je zagaye 44 kafin aka samu shugaban majalisa saboda bambancin ra'ayi.

Sabon Shugaban majalisar zai fuskancin kalubalen hada kan yan jam'iyyar kafin babban zabe.