Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Hughton ke cikin tsaka-mai-wuya domin farfaɗo da tawagar Ghana
- Marubuci, Daniel Dadzie and Nishat Ladha
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- An wallafa
Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Ghana Chris Hughton ya ce "zai koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya" yayin da ake ta ce-ce-ku-ce game da makomarsa a tawagar Black Stars gabanin fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Fifa na 2026.
Hughton, wanda ke shirya ƙungiyar domin buga wasa da Madagascar da Comoros, yana fuskantar matsin lamba tun bayan da tagawar ƙasar ta yammacin Afirka ta sha kashi a hannun Mexico da ci 2-0 da kuma 4-0 a Amurka a wasannin sada zumunta da suka yi a watan jiya.
Duk da raɗe-raɗin da ya yawaita, kocin mai shekaru 64 ya ce hankalinsa ya karkata ne ga aikin da ke gaba.
Tsohon kocin Brighton da Newcastle ya shaida wa BBC cewa "Ni a matsayina na koci aikina ne in koyi darasai daga yadda ƴan wasanmu ke wasa da kuma yadda za mu inganta, saboda yanzu muna buga wasannin gasa - wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya."
"Wasanni biyu ne da dole ne mu taka rawar gani.
"Ayyukana a matsayina na kocin Black Stars shi ne samun sakamako mafi kyau da kuma mafi kyawun ƙokari daga ƙungiyar. Ba koyaushe za ka iya samun hakan ba.
"Amma za ka iya ɗaukar darasi a koyaushe daga abubuwan da suka faru a baya, ko da abu ne mai kyau ko kuma mara kyau. Kuma, a ƙarshe, zan yi aiki tuƙuru kamar yadda koyaushe nake yi don ƙoƙarin samun sakamakon mafi inganci."
Hughton ya dawo da kyaftin ɗin Ghana Andre 'Dede' Ayew - wanda ba ya cikin ƴan wasan da suka kara da Mexico da Amurka - Hughton ya kira shi don buga wasa da Madagascar a gida a ranar 17 ga watan Nuwamba da kuma zuwa Comoros kwanaki huɗu bayan haka.
Ayew, mai shekaru 33, har yanzu ba shi da kulob tun bayan barin Nottingham Forest a ƙarshen kakar wasan da ta gabata.
Duk da haka, shi ya zama kyaftin ɗin Black Stars a gasar cin kofin duniya a Qatar 2022, inda Ghana ta fice a matakin rukuni, kuma Hughton ya ce ɗan wasan na da muhimmanci a tsarin ƙasa.
Kocin ɗan ƙasar Ireland ya ƙara da cewa "Dede Ayew har yanzu ɗan wasa ne mai matukar kyau kuma har yanzu mutum ne da zai iya zama mafi kyawun ɗan wasa a wajen atisaye."
"Shi mutum ne wanda ke da matuƙar mahimmanci saboda shi ne kyaftin - yana da matukar tasiri ga matasan ƴan wasan da ke cikin tawagar. Don haka ba wai don hazaƙarsa ta buga wasa ne kawai ba, don tasirin da zai iya yi ne ga tawagar baki ɗaya."
Ghana za ta kuma kara da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Chadi domin samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2026, inda wadda ta kasance jagorar rukunin za ta sami tabbacin shiga gasar da za a buga a Canada da Mexico da kuma Amurka.
Ko ya kamata Black Stars su yi tunanin Afcon yanzu?
A ranar 13 ga watan Janairu ne za a fara gasar cin kofin Afrika a ƙasar Ivory Coast, inda magoya bayan Ghana ke matuƙar son ganin sun samun nasara.
Black Stars dai ba ta lashe kofin da ake so ba tun a shekarar 1982, wanda shi ne na ƙarshe cikin guda hudun da ta taɓa ci, kuma yanzu an haɗa su da Masar da Cape Verde da kuma Mozambique a rukunin B.
Sai dai Hughton ya ce dole ne ƴan wasansa su mayar da hankali kan fara yaƙin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a mako mai zuwa.
"Yana da kyau a yi magana game da Afcon, amma wani lokacin ga masu horaswa yana da wahala saboda muna da wasanni biyu masu mahimmanci kafin lokacin," in ji shi.
"Ina ganin idan hankalinku ya karkata sosai, za ku iya kawar da idanunku daga kan abin da ke gabanku a wannan lokacin mafi mahimmanci - wasanninmu na cancantar shiga gasar cin kofin duniya.
"Abin da za mu so shi ne mu yi ƙoƙari a waɗannan wasannin, mu samu nasara a wasannin kuma mu samu damar shiga Afcon da kyakkyawar yanayi. Amma dole ne wannan (wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya) su kasance kan gaba."
Dangane da Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka kuwa, Hughton na sa ran zai fuskanci ƙalubale mai tsanani daga ƙasashe da dama a Ivory Coast.
Ya ƙara da cewa "Morocco da Egypt da Senegal da Cameroon da Tunisia - a halin yanzu, ƙungiyoyin da suke taka rawar gani a Afirka - da kuma gasar cin kofin Afrika - kamar yadda ba a taɓa gani ba."
"Akwai ƙarin ƴan wasa da yawa a manyan ƙungiyoyi a Turai da kuma a fagen duniya wanda hakan ke sa gasar Afcon ta zama mai wahala ga kowa da kowa, kuma ta kasance mafi ban sha'awa ga kowa.
"Muna da tarihi mai ban sha'awa kuma duk inda ka je kuma ka yi magana game da Black Stars, ƙasa ce kuma tawagar ƙwallon ƙafa da aka sani a duniya. Kuma babu shakka, wannan ya faru ne sakamakon tarihin Black Stars."
Rikici tsakanin kulob da ƙasa kan Afcon
Ghana, kamar mafi yawan ƙungiyoyin da za su taka leda a gasar cin kofin Afirka a farkon shekara mai zuwa, suna da ƴan wasa da dama da ke taka leda a wasu manyan ƙungiyoyin Turai.
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Thomas Partey da Mohammed Kudus na West Ham da kuma ɗan wasan gaba na Crystal Palace, Jordan Ayew duk za su bar ƙungiyoyinsu na Firimiya domin buga gasar a Ivory Coast, amma Hughton ya ce ƴan wasansa sun mayar da hankali sosai wajen wakiltar ƙasarsu.
"Ban ga wani abu da zai nuna cewa ba su da cikakkiyar himma ba. Yanayin da muke gani a sansanin yana da ban sha'awa," in ji shi.
"Kuma ina da ƙwarin gwiwa cewa duk wanda ya fito don Black Stars yana nan saboda yana so ya kasance a wurin kuma yana son ya yi iyakacin ƙoƙarinsa."
Hughton yana da yaƙinin cewa masu horar da ƴan wasa a duk fadin Turai yanzu sun fi yarda da lamarin kuma kulob din da ya gabata da na kasar ya mutu.
“Mafi yawan kungiyoyi, da masu horas da ‘yan wasa, yanzu sun san da cewa idan suka ɗauki ɗan wasan Afrika akwai damar da za su iya rasa shi na wani lokaci don gasar cin kofin ƙasashen Afrika.
"Don haka abu ne da ba sabon ba kuma ina tsammanin kulob na zamani da mahukuntan ƙungiyoyi na zamani sun san da cewa hakan zai faru."