Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ghana a Qatar: Girman abubuwan da suka faru a tarihi na shafar gasar cin Kofin Duniya
A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridun Afirka, wata marabuciya 'yar kasar Ghana, Elizabeth Ohene ta bayyana cewa fata da kuma burin kasar, hade da tarin jakunkunan kaya sun rataya a wuyan 'yan wasan kwallon kafarta.
'Yan wasan kwallon kafa na Ghana Black Stars, sun samu cancantar zuwa Qatar nan gaba cikin wannan shekarar amma da alama hakan zai yi tasiri kan wasu abubuwa da suka faru a tarihin gasar cin Kofin Duniya.
Tabbas mun san cewa samun galaba a ko da yaushe na tafe tare da shan kashi. Dole sai ka bai wa wani kashi kafin ka samu galaba. Wani yanayi na "galaba da galaba" da mutane ke magana a kai babu shi a rayuwar gaske, kuma ko shakka babu har ma da cikin filin wasan kwallon kafa.
Wani lokaci abubuwan da kake nuna murna a kai ba sosai ba ne don cewa saboda ka samu galaba, amma don kawai ka bai wa wani kashi ne.
Mu a kasar Ghana mun san mene ne shan kaye. Idan kuna bibiyar Black Stars, 'yan wasan kwallon kafarmu, za ka fahimci wani abu game da rayuwa cikin bacin rai.
'Hawan jini'
Wannan kungiyar wasan kwallon kafa ce da masu tsananin goyon bayanta suke kallon buga wasan a cikin akwatunan talabijin ido rufe.
Don haka bibiyar gasar wasannin baya-bayan nan na samun galabar shiga gasar cin Kofin Duniya, fuskantar wani abu ne mai kara haifar da hawan jini.
Daga karshe, dole sai mun kayar da Afirka ta Kudu da Najeriya kafin mu samu hanyar wucewa zuwa Qatar. Kundin tattara bayanai zai nuna cewa karawa ta biyu na neman zama zakara tsakanin Afirka ta Kudu Ghana ya faru ne a nan kasar Ghana inda yin kunnen-doki ba zai yi wani amfani ba - dole sai mun kayar da su - kuma mun kayar da su din.
Har yanzu 'yan wasan Afirka ta Kudu na kokarin murmurewa daga wancan shan kayen, bayan da suka yi ta kokari amma suka gaza sa Fifa ta sauya sakamakon a bisa dalilan da suka bayyana wasu "matakan rashin nuna dattaku" daga alkalin wasan.
Lokacin da Ghana ta samu cancantara lokacin shiga gasarta ta farko ta cin Kofin Duniya kan ta tafi kasar Jamus a shekarar 2006, Afirka ta Kudu ce ta zamana dole mu kayar, kuma mun samu yin hakan a birnin Johannesburg, a cikin karo na biyu na buga wasannin biyu.
Wannan karon, 'yan wasan Afirka ta Kudu ba su dauki kayen da suka sha da wasa ba, kana sun hada kai wajen ganin cewa mun sha kaye a hannun Najeriya.
A can filin wasan Abuja a bugawar karshe da Najeriya, mun rika jin addu'oin hadin gwiwa na 'yan Afirka ta Kudu da Najeriya a kanmu. Amma mun tsallake muka zama zakaru.
Idan kai dan kasar Ghana ne, babu wani abu da yafi bakin ciki kamar shan kaye a gasar wasan wallon kafa a hannun Najeriya. Kuma mun san cewa ga 'yan uwanmu 'yan Najeriya, shan kaye a buga wasan da Ghana ba ma abin bakin-ciki kadai ba ne - abin tayar da hankali ne.
'Yan Najeriya za su iya shan kaye daga hannun kowa, amma a hannun Ghana ba abin da za su iya jure wa ba ne. Zan iya cewa muna ji tare da fahimtar bakin-cikin su.
Muna kuma da wata jikakkiya a baya da sauran abokan karawarmu biyu na tawagar Group H.
Ta yaya kuwa duk wani dan kasar Ghana zai iya mancewa da kasar Uruguay kan dan wasan nan Luis Suarez a gasar wasan cin Kofin Duniya na shekarar 2010 a Afirka ta Kudu? Muna gab da samun galabar shiga gasar kusa da na karshe ne lokacin da Suarez ya naushi kwallon ta fita wajen ragar.
Lokaci ne kuma na sanannen wasan gaza samun nasarar bugun fenareti da dan wasanmu mai kyau Asamoah Gyan ya yi, wasan da daga karshe muka rasa samun galaba a hannun kasar Uruguay a bugun fenareti. Yanzu za mu sake haduwa da su a matakin rukuni a Qatar.
Ita ma kasar Portugal na cikin tawagar 'yan wasan Group H amma ba tauraron dan wasanta Cristiano Ronaldo ne ya rika daukar hanula a nan ba. Wasan karshe da Ghana ta buga da Portugal na cin Kofin Duniya a kasar Brazil ne a shekarar 2014 - wasan da bai kamata a ce mu rika tunawa da shi ba.
Lokaci ne da Ghana ta yi kaurin suna, ba saboda kwallon kafa ba, amma saboda dalilai marasa dadi. Tawagar 'yan wasanmu sun daura damarar buga wasa da Portugal lokacin da ta bayyana cewa 'yan wasanmu na da matsalar da ta shafi wa'adin karshe, da kin amincewa da yin wasa har sai sun ga - kana sun rike a hannunsu - kudaden alawus da aka yi musu alkawari.
Dole sai da gwamnatin kasar Ghana ta yi hayar jirgin saman da ya dauki kudaden daga birnin Accra zuwa kasar Brazil.
Bari mu ce wannan ba lokaci ne na wani abin alfahari ga kasarmu ko 'yan wasanmu ba.
Babu wani abin mamaki a ciki, bayan da kasar Brazil ta bai wa Black Stars sun rasa samun goyon bayan 'yan kasar Ghana da dama. Amma kuma tuni komai ya wuce.
Ko shakka babu hakan ya taimaka wajen ganin mun samu cancantar shiga gasar wannan shekarar ta cin Kofin Duniya a Qatar bayan samun galaba a kan Najeriya. Hakan na nufin cewa : "An yafe muku, Black Stars, ku cigaba da wasa - muna kaunar."
Ina na yakinin ko 'yan Afirka ta Kudu da 'yan Najeriya za su jinjina tare da taya ku murna a Qatar.
Da zarar sun fara buga wasan da Portugal, ko Uruguay ko Korea ta Kudu, ba za su iya kassara tarihin da ya hada kawunanmu wuri guda ba.