Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abinda kuke son sani kan wasan Bayern Munich da Arsenal
Bayern Munich da Arsenal za su buga wasa na biyu a quarter final a Champions League ranar Laraba a Allianze Arena.
Kungiyoyin sun tashi 2-2 a makon jiya ranar Talata a Emirates a gasar ta zakarun Turai.
Arsenal na fatan kai wa zagayen daf da karshe a Champions League karon farko tun bayan shekara 15, wadda ba ta taba daukar kofin ba.
Bayern ta kai daf da karshe a Champions League a 2020, kakar da ta lashe kofin kuma na shida jimilla.
Bayanai kan 'yan wasan kungiyoyin:
Ana tantama kan koshin lafiyar Odegaard da kuma Saka, yayin da mai tsaron bayan Arsenal, Jurrien Timber ya dade yana jinya.
A Bayern Munich kuwa, an dakatar da Alphonso Davies, bayan da ya karbi katin gargadi uku a gasar ta zakarun Turai.
Wadanda ke jinya a kungiyar sun hada da Serge Gnabry da Leroy Sane da kuma Kingsley Coman.
Bayanai kan wasa tsakanin kungiyoyin:
Bayern Munich ta kai zagayen gaba sau biyu daga uku a gasar zakarun idan ta je waje ta tashi 2-2.
Bayern Munich da Barcelona sun fitar da Arsenal karo hudu kowacce a zagayen karawa gida da waje a gasar zakarun Turai.
Kungiyar Bayern Munich
An yi waje da Bayern a Champions League zagayen quarter-finals a kaka uku baya a wasa da Paris St-Germain a 2020-21 (karkashin Hansi Flick), 2-1 gida da waje da karawa da Villarreal a 2021-22 (karkashin Julian Nagelsmann) 4-1 gida da waje da wasa da Manchester City a 2022-23 (karkashin Thomas Tuchel).
Watakila Bayern ta zama ta biyu da za a fitar a zayaen quarter final a Champions League karo hudu a jere, bayan Paris St-Germain daga 2012-13 to 2015-16.
Rabonda Bayern Munich ta haura quarter finals a Champions League tun bayan da ta doke Barcelona 8-2 a Lisbon a 2019, wadda daga baya ta lashe kofin.
Kungiyar Arsenal
Arsenal ba ta yi nasara ba a karawa takwas a Champions League da ta buga a waje a zagayen quater final da canjaras hudu aka doke ta wasa hudu.
Wannan shi ne wasa na biyu da Mikel Arteta zai ja ragamar quarter final a gasar zakarun Turai a matakin koci, bayan nasara a kan Slavia Prague a 2020-21 a Europa League.
Wasa biyu ne Arsenal ta haura quarter finals daga shida a Champions League, wanda ta yi nasara a kan Juventus a 2005-06 da kuma a kan Villarreal a 2008-09.