Ko mai zai faru a Champions League ranar talata da Laraba?

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata da Laraba za a karkare wasannin daf da na kusa da na karshe a Champions League, domin samun masu buga daf da karshe.
Za a buga wasa biyu ranar Talata, sannan a kara yin wasu biyun ranar Laraba, domin tantance wadanda za su kai zagayen gaba.
Ranar Talata Borussia Dortmund da Atletico Madrid.
Atletico Madrid ce ta yi nasara 2-1 a wasan farko a Spain.

Asalin hoton, Getty Images
Antoine Griezmann ya taka rawar gani da Atlético Madrid ta ci Dortmund a wasan farko, inda mai shekara 33 ya karbi kyautar gwarzon karawar ta daf da na kusa da na karshe.
Kungiyar da Diego Simone ke jan ragama ya kwan da sanin da jan aiki a gabansu, kamar yadda suka fuskanci kalubale a wasan farko.
Tuni koci, Edin Terzic ya yi sauyin 'yan wasa uku domin ya samu damar kai wa zagayen daf da karshe a Champions League.
Sébastien Haller ya ci kwallo mai kayatarwa, yayin da Jamie Bynoe-Gittens da Julian Brandt suka buga kwallo ya bugi turke kowannensu.
Haller ya ci kwallo 12 daga karawa 13 a Champions League.
Ranar Talata Barcelona da Paris St Germain
Paris St Germain ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-2 a wasan farko a Faransa.

Asalin hoton, Getty Images
A karawar ce Lamine Yamal ya zama matashin da ya buga Champions League a tarihi mai shekara 16 da kwana 272.
Yana da kyau yaro ya fara kwallo da wuri, kenan a wasa na biyu a Spain ana sa ran Yamal zai kara kwazon da zai kai Barcelona zagayen daf da karshe a Champions League.
Andreas Christensen wanda ya shiga karawar daga baya ya kuma ci kwallo, ba zai buga wasa na biyu ba sakamakon hukuncin dakatarwa tare da kyaftin, Sergi Roberto mai jinya a karawar da za a yi a Estadi Olímpic Lluís Companys.
Ita kuwa Paris St Germain za ta samu kwarin gwiwa bayan da Achraf Hakimi zai yi mata wasan, bayan da ya gama hukuncin dakatarwa - sannan Kylian Mbappe zai je Spain, kasar da zai koma taka leda a badi a Real Madrid - kenan zai kara nuna kansa duk da ba wannan ne karon farko da zai fuskaci Barcelona ko zuwa Spain ba.
Ranar Laraba Bayern Munich da Arsenal
Arsenal da Bayern Munich sun tashi 2-2 a wasan farko a Emirates.

Asalin hoton, Getty Images
Alphonso Davies ba zai yi karawar ba, bayan da yake hukuncin dakatarwa, shi kuwa Serge Gnabry na jinya - kenan lallai Bayern na bukatar wadanda za su kular mata da Ben White da Bukayo Saka, wadanda suka taka rawar da Arsenal suka tashi 2-2 a Emirates.
Watakila Bayern ta yi amfani da Raphaël Guerreiro da kuma Kingsley Coman.
Bayern na fama da kalubale a bana musammam a Bundesliga, wadda Bayern Leverkusen ta karbe a hannunta a bana, bayan daukar 11 a jere.
To sai dai tana taka rawar gani a Champions League, Harry Kane ma na taka rawar gani, amma Thomas Muller zai yi wasa na 150 idan ya buga karawar ranar Laraba.
Shi kansa Manuel Neuer na fatan hana kwallo ya shiga ragarsa karo na 58.
Ranar Laraba Manchester City da Real Madrid
A wasan farko a Spain sun tashi 3-3 a Madrid, kenan komai zai iya faruwa a Etihad, kowacce kungiya tana da damar kai wa zagayen daf da karshe.

Asalin hoton, Getty Images
A bara City da Real sun tashi 1-1 a Spain, sannan aka doke Real Madrid 4-0 a Etihad. a Champions League, hakan ya kai ga City ta dauki kofin a karon farko a tarihi.
City kan ci kwallo uku a kowanne wasa tara a Champions League a bana da yin rashin nasara daya daga fafatawa 13 a gasar zakarun Turai da ta fuskanci kungiyar Spain.
Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta ci ta Spain wasa takwas da canjaras hudu, yayin da Bernardo Silva ya ci kwallo hudu daga karawa biyar da ya fuskanci Real Madrid.
To sai dai Real Madrid mai Champions League 14 jimilla tana da kwarewar buga kofin, wadda ke daf da lashe La Liga na kakar nan.











