Michael Oliver ne zai busa wasan Braga da Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Hukumar kwallon kafa ta Turai ta bayyana Michael Oliver a matsayin wanda zai yi alkalancin wasan Champions League tsakanin Braga da Real Madrid.
Ranar Talata Real Madrid za ta ziyarci Braga domin buga wasa na uku a cikin rukunin gasar Zakarun Turai ta bana.
Wannan ne karo na uku da rafalin dan kasar Ingila zai busa wasan da ya shafi Real Madrid.
Wasan karshe da ya busa a wasa da Real Madrid shi ne wanda ta doke Eintranch Frankfurt 2-0 a European Super Cup a 2022.
Kafin nan, ya fara busa wasan da Juventus ta doke Real Madrid 3-1 a wasa na biyu a daf da na kusa da na karshe a gasar 2017/18.
Wasannin da za a buga ranar Talata 24 ga watan Oktoba:
- Inter Milan da Red Bull Salzburg
- Galatasaray da FC Bayern Munich
- Manchester United da FC Kobenhavn
- Sevilla da Arsenal
- RC Lens da PSV Eindhoven
- FC Union Berlin da Napoli
- Sporting Braga da Real Madrid
- Benfica da Real Sociedad




