Arsenal za ta fafata da Man City a kofin Community Shield

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta yi niyyar tabbatar da cewa za ta iya sake kalubalantar Manchester City a gasar Premier yayin da kungiyoyin biyu za su kara a gasar Community Shield ranar Lahadi.
Ana buga wasan Community Shield ne tsakanin wadanda suka yi nasara a gasar Firimiya da kuma wadanda suka lashe kofin FA, amma kungiyar Pep Guardiola ta lashe duka kofunan a kakar wasan da ta gabata - da kuma gasar zakarun Turai.
Arsenal ta jagoranci teburin gasar Firimiya na tsawon kwanaki 248 a kakar wasa ta 2022-23, lokaci mafi dadewa ga wata kungiya da ta kasa lashe gasar a tarihin gasar ta Ingila.
Yunkurin nasu ya faskara yayin da City ta farfado ta tsere musu, inda gajiya da raunuka suka addabi 'yan wasan Arsenal.
Magoya bayan kungiyar za su so ganin an yi gagarumin yunkuri a kasuwar cinikin 'yan wasa ta bazara don tabbatar da kalubalen kakar da ta wuce ba zallar sa'a ba ce, kuma tabbas kungiyar ta yi hakan.
Dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice, shi ne fitaccen dan wasan da Arsenal ta dauko daga West Ham a kan fan miliyan 100.
Zuwansa ya biyo bayan daukar dan wasan Jamus Kai Havertz daga Chelsea kan fan miliyan 65, da kuma dan wasan baya na Netherlands Jurrien Timber daga Ajax kan kudin da zai kai fam miliyan 38.5.

Asalin hoton, Getty Images
A nata bangaren kuma, Manchester City ta dauko 'yan wasa biyu masu mahimmanci a wannan bazara, inda ta kammala dauko dan wasan tsakiya na Croatia, Mateo Kovacic daga Chelsea kan fan miliyan 25, sai kuma abokin wasansa na kasa, Josko Gvardiol, kan fan miliyan 77 daga RB Leipzig.
City ta lashe gasar bara da tazarar maki biyar tsakaninta da Arsenal, don haka ba ta bukatar karfafawa kamar Gunners din, duk da cewa ta yi rashin kyaftin dinta Ilkay Gundogan.
Dan wasan ya taka rawar gani sosai da City ta lashe manyan gasa uku, inda ya zira kwallaye 11 a wasanni 52, kuma duk da an yi masa tayin sabon kwantiragi a filin wasa na Etihad, ya zabi komawa Barcelona.
City ta sha kashi a hannun Leicester da Liverpool a kakar wasa biyun da suka wuce, amma ba a cire tsammanin cewa za su iya nasara kan Arsenal a wasan bana.
Sai dai kuma komai na iya faruwa.











