Wasu Zaɓaɓɓun hotunan Afirka na mako tare da hotunan 'yan nahiyar a wasu sassan duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan matar ta ɗauki hoto a cikin ɗakinta a garin Kibera na ƙasar Kenya ranar Lahadi. Ana tunanin cewa ƙawata ɗakuna na daga cikin abubuwan da ke kawar da hankulan matasa daga faɗawa tarkon shaye-shaye da sauran miyagun laifuka.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Suma waɗannan matasa sun ɗauki hoto tare da jita a ɗakinsu a unguwar -wadda babban unguwa ce a birnin Nairobi.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Cincirindon mutane ne suka taru domin tarbar Fafaroma Fransis a birnin Kinshasa na ƙasar Jamhuriyar Dimokradiyya Kongo Ranar Laraba.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka saurari huɗubar da ya gabatar mai taken ‘yafe wa maƙiya’. Ya gabatar da jawabin ne a daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ke fama da rikicin cikin gida a yankin gabashin ƙasar tsakanin sojojin gwamnati da masu tayar da ƙayar baya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Fafaroman ya yi kwana uku a DR Kongo kafin ya isa ƙasar Sudan ta Kudu ranar Juma’a.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mutane da dama ne suka taru don yin maraba da fafaroman ciki har da waɗananna ƙananan yaran sanye da fararen tufafi.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wani mutum sanye da tufafin gargajiya na ƙasar Senegal a wani bikin al’ada mai suna bikin Kankurang a garin janjanbureh.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani yaro ke ƙoƙarin kama tattabara a a lokacin da take tashi a kusa da masallacin Abu al-Hajjaj a ƙasar Masar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan matar ke yanka tumatir domin busar da shi a birnin Luxor na ƙasar Masar ranar Litinin. Tana aiki ne a kamfanin buar da tumatir na ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Waɗannan matasan na rawa gabanin buɗe gasar kofin duniya na ƙungiyoyi da ake gudanarwa a ƙasar Morocco, inda ƙungiyar Al Ahly ta Masar ta doke Auckland City ta ƙasar New Zealand da ci 3-0.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Idan muka koma ziyarar da Famaroma yake yi a ƙasashen Afirka, wannan matar na goge kayanta a birnin Juba na ƙasar Sudan ta Kudu a shirye-shiryen tabar fafaroman.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, A birnin Legas na Najeriya inda wannan malamar makarantar ke koya wa ɗailibai karatu a unguwar Mokoko ranar Juma’a.