Arsenal na zawarcin ɗan wasan tsakiyan Royal Antwerp

An wallafa

Arsenal za ta iya kai tayin fam miliyan 13 kan ɗan wasan tsakiya na Royal Antwerp Arthur Vermeeren a watan Junairu.

Matashin ya taka rawar gani a Antwerp wanda hakan ya sa ɗan wasan ya ja hankalin manyan ƙungiyoyi a Turai tare ciki har da Barcelona, amma rahotanni na bayyana cewa Arsenal ce kan gaba wurin zawarcin ɗan wasan.

Kwanan nan an ba da rahoton cewa Mikel Arteta na shirin ɗaukar sabon ɗan wasan tsakiya don sauya wa Declan Rice yanayin wasansa.

Duk da haka, ɗan wasan tsakiyar har yanzu matashi ne kuma yana buƙatar lokaci don bunƙasa ƙwarewarsa.

Arsenal ta fara kakar wasan bana da ƙafar dama a gasar Premier, amma yanzu an fitar da ita daga gasar cin kofin Carabao bayan ta sha kashi a hannun West Ham United ranan Larabar da ta gabata.

Za ta yi sha'awar komawa kan hanyar samun nasara a lokacin da ta ziyarci St. James Park don karawa da Newcastle United a gasar Premier a ƙarshen mako.