Shekarata 23 ina koyarwa ba tare da albashi ba - Malamar makaranta

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Chérif Ousman MBARDOUNKA
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journaliste - BBC Afrique
- Aiko rahoto daga, Dakar
- Marubuci, Jean Charles Biyo'o Ella
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Correspondant BBC Afrique
- Aiko rahoto daga, Yaoundé
- An wallafa
An kwashe shekaru masu yawa ana ta kiraye-kirayen duba matsalar barin aikin malunta da matasa ke yi saboda rashin tallafi da ci gaba da sauran matsaloli.
A wannan shekara alƙaluman matasan da ke barin aiki ya zarta hasashen da gwamnatin ƙasar ta yi, a yunƙurinta na rage alƙaluman kamar yadda ta alƙawarta.
Malaman makarantun Furamare da na Sakandire a Kamaru na dab da shafe shekarar karatu ta 2023/2024 cikin yanayin yajin aiki.
Kungiyoyin kwadagon ƙasar sun daɗe suna ta kiraye-kirayen magance matsalar yajin aikin, ta hanyar biyan malamai basukan da suke bin gwamnati.
Ƙungiyoyin sun ce suna sane da irin taskun da malaman makaranta ke fuskanta a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.
Abin da ke ƙara ta'azzara wannan abu cikin shekaru masu yawa shi ne "kusan malaman sakandire 40,000 da aka yaye daga makaratun horon malamai cikin shekaru goma da suka gabata ba su taɓa samun albashi ba, kamar yadda wani kiyasi mai zaman kansa da aka gabatar.
Hakan ya sanya bashin da suke bin gamnati ya kai kusan saifa biliyan 180, kamar yadda wani kiyasai da kungiyar OTS ta gudanar.
Tun watan Fabrairun 2022 ne malaman ke rigima da hukumomi kan biyansu haƙƙoƙinsu, inda suke buƙatar a biya su wani ɓangare na bashin da suke bi, tare da buƙatar bai wa malaman makaranta wani matsayi na musamman cikin al'umma, ko ma shirya wani babban taron ƙasa kan ilimi.
“Shekara 23 ba tare da albashi ba”

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“Shekarata 23 ina koyarwa ba tare da albashi ba, ko ƙarin girma”,
Olivia Manekeng, mai shekara 44, na ɗaya daga cikin mutanen da ke fama da sana'ar koyarwa a Kamaru. "Na fara aikin koyarwa a shekarar 2001", in ji malamar makarantar.
A lokacin, a matsayin malamar reno, kafin na samu takardar shaidar malunta ta CAPIEM.
"A shekarar 2007 na yanke shawarar shiga makarantar hoon malamai ta ENIEG, inda na samu horon shekara uku, na kammala a shekarar 2010".
Ta ƙara da cewa "Daga wannan shekara har ya zuwa yau, ba a taɓa yi mini karin girma ba, duk kuwa da sadaukarwar da na yi da kuma kwarewata".
Olivia, mai 'ya'ya huɗu - wadda a yanzu ba ta da aure, kaka ce ga yaro ɗaya da 'yarta ta haifa sakamakon fyaɗen da aka yi mata a shekarar 2019 - na daga cikin malaman makarantar da ke fama da rayuwa sakamakon rashin albashi.
“Duba da wannan nauyi da ke kaina kuma ba tare da samun albashi ko ƙarin girma ba, a makonnin da suka gabata ne na yanje shawarar hakura da aikin na koyarwa. Dole mu nemi wani abin yi , domin ciyar da 'ya'yan da kuma jikana".
Rayuwa ba kawai hidimta wa jama'a ba ne, "ya kamata a sake nazarin yanayin da malaman firamare da na sakandire ke ciki a Kamaru"
A shekarar da ta gabata, labarain Haminou ya girgiza duniya. Wani malami ne a makarantar Babbar Sakandiren Beka da ke yankin arewa mai nisa a ƙasar, ya mutu ne bayan shafe shekara 10 ba tare da albashi ba.
Yunƙurin da gwamnati ke yi
A ƙarshen watan Satumba, Ministan Ilimi a matakin farko na ƙasar, Laurent Serge Etoundi a gaban manema labarai da abokansa da ma'aikatan gwamnati ya ƙaddamar da wani shirin gwamnati da zai riƙa ɗaukar ɗaliban da aka yaye - a manyan makaratun ƙasar - aikin gwamnati kowace shekara.
Ya kuma alƙawarta yin duk abin da ya dace wajen magance matsalar biyan albashi ga malaman makarantar ƙasar.
Ya ce gwmanati na sane da matsalar tana kuma yin duk mai yiwuwa domin maganceta.
A Kamaru matakan da ake bi wajen ƙara wa malaman makarantun Firamare girma na da tsarƙaƙiya.
Lamarin da ya sanya shi zama mai matuƙar wahala, idan aka kwatanta na da makarantun sakandire da sauran manyan makarantu.
A matakin firamare, bayan kammala shekarun samun horo a makaranta, dole malamai su rubuta jarrabawar neman ƙarin girma, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta tsara kafin a dauke su aiki.
Bankin Duniya kan ɗauki nauyin ɗaukar malaman a wasu lokuta. A shekarar 2022, cibiyar 'Bretton Woods' ta kashe saifa biliyan 54 wajen ƙara wa malamai 3,000 girma.
Amma a hukumar da ke kula da makarantun sakandire da ke lura da manyan makarantun sakandire da matsakaita, tsarinta ya bambanta dangane da ƙarin girma.
A nan daliban da suka kammala samun horo a makarantu ba za a yi musu jarrabawar ƙarin girma kafin daukarsu aiki ba.
Dalilin maƙalewar albashi da ƙarin girman

Asalin hoton, Mouvement OTS
Sakamakon rashin martani daga gwamnati kan buƙatun malaman, ya sa suka ci gaba da yajin aikin da suke yi.
Aristide Mono wani mai bincike kan harkokin aikin gwamnati a ƙasar, ya ce "yajin aikin ya ci gaba sakamakon rashin kulawar gamnati"
"In ba yanzu ba gamnati ba ta taɓa nuna cewa da gaske tana da sha'awar magance matsalar".
Tun bayan fara yajin aikin, ministan cikin gida na ƙasar, Paul Atanga Nji, ya umarci gwamnonin jihohin ƙasar ta su gano tare da gudanar da bincike kan shugabannin kungiyar OTS.
Paul Atanga Nji ya alakanta matalar da ƙungiyoyin kwadago waɗanda ya kira 'marasa alƙibla' da ke neman 'wargaza' ƙasar.
An martaba umarnin ministan a wasu sassan ƙasar, inda aka riƙa kama malaman makarantar da ke yajin aikin, ko a sauya musu wuraren aiki zuwa wurare masu nisa, a wani yunƙuri na daƙile yajin aikin.
A yankin Adamaoua, ranar 13 ga watan Satumba, wakilin daga hukumar ilimin sakandire sahen Vina, Mohaman Bello ya aike da takardun buƙatar rubuta jarrabawar ƙwarewa ga malamai 45 daga makarantu 22 da ke ƙarƙashin kulawarsa.
Ire-iren waɗannan barazana da hukumomi ke yi wa malamai ya taimaka wajen ƙyamar aikin koyarwa a ƙasar.
Inda malaman suka ɓullo da sabuwar hanyar bayyana buƙatunsu ga gwamnati, domin kauce wa fushin hukumomi a kansu.
A yanzu malaman kan shiga azuzuwa, sai dai ba sa koyarwa, a maimakon haka sai su riƙa yi wa ɗaliban bayanin dalilinsu na ɗaukar matakin rashin koyarwa.











