Zargin kafa gwamnatin riƙo a Najeriya abin fargaba ne - Jam'iyyu

...

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya ce zargin kafa gwamnatin riƙo a ƙasar, babban abin tayar da hankali da cusa fargaba ne.

Shugaban kwamitin, Engr Yabagi Sani ya ce “Ba ma mu ‘yan siyasa ba kaɗai, duk wanda ke da kishin Najeriya, yake da kishin ci gaban Najeriya, yake kishin dimokraɗiyya ta kafu a Najeriya.

Idan aka dubi matsayin Najeriya, ba kawai a Afirka ba, a duniya ma gaba ɗaya, abin da DSS ta fito da shi, abu ne na fargaba”.

Engr. Sani na mayar da martani ne kan tabbatacin da DSS ta yi cewa gaskiya ne raɗe-raɗin da ake yi cewa wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na kitsa maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya don hana rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, nan gaba cikin watan Mayu.

Ya ce a ganinsa, abin da ya janyo kitsa irin wannan maƙarƙashiya da ake zargi, shi ne rashin gamsuwar da mai yiwuwa wasu ‘yan siyasa ke da ita, game da zaɓukan 2023 da aka kammala a baya-bayan nan.

"Lallai waɗanda ba su gamsu ba ne da abin da hukumar zaɓe ta fito da shi, mai yiwuwa cikinsu ne aka samu waɗanda ke nuna fushinsu," in ji Engr Sani.

Engr Yabagi Sani ya ce alhakin hukumar DSS ne ta ɗauki mataki, kuma ta fito ta yi wa jama’a bayani game da binciken da ta gudanar, da kuma abin da ta gano saboda ta san girman illar da irin wannan maƙarƙashiya za ta iya haddasa wa dimokraɗiyyar Najeriya.

A cewarsa, irin wannan zargi idan aka samu waɗanda ke yunƙuri ko kuma suna cikin aikatawa, to ya kamata a ɗauki mataki, ba wai a fito a bayyana wa jama’a ba.

“Idan an gaya wa jama’a, to me za su yi?” Yabagi ya tambaya.

Ya ce tun da DSS ta yi iƙirarin cewa ta san ‘yan siyasar da ke kitsa wannan maƙarƙashiya, to kamata ya yi idan lokaci da halin a faɗa wa jama’a ya yi, sai ta fito ta bayyana sunayen mutane da ke shiryawa da kuma matakin da ta ɗauka a kan su.

“To ta nan ne jama’a za su yarda.

Amma yanzun in ba a yi hankali ba, za a ma ce su DSS ɗin nan me suke nufi da irin wannan magana da suka yi?”

Da aka tambaye shi ko yana da masaniya kan wannan shiri na kafa gwamnatin riƙo da DSS ta yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa irinsa na kitsawa, sai shugaban kwamitin gamayyar jam’iyyun Najeriyar ya ce “A’a, wannan ai kamar ana so a shafa wa ‘yan siyasa kashin kaji ne kawai.

Idan gaskiya ne a fito a gaya mana cewa su wane kaza ne, kuma ga abin da suka yi."

"Shi ya sa na ce, mu ba mu yarda da wannan ba. Su fito su gaya wa jama’a ƙarara cewa ga abin da yake faruwa”.

Wanne zargi DSS ta yi?

A ranar Laraba ne hukumar jami'an tsaron farin kaya ta Najeriya ta tabbatar da raɗe-raɗin cewa akwai wata ƙullaliya da wasu 'yan siyasa ke kitsawa don ganin an kafa gwamnatin riƙo a ƙasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta ce “wani yunƙuri ne na jingine tsarin mulkin Najeriya, da yin zagon ƙasa ga mulkin farar hula da kuma yunƙurin jefa ƙasar cikin ruɗani.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “masu kitsa lamarin sun tattauna kan hanyoyi da dama na aiwatar da shirin nasu, kamar haddasa mummunar zanga-zanga a manyan biranen Najeriya, wadda za ta janyo a ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci.”

“Ko kuma ta hanyar nemo umarnin kotu don a dakatar da rantsar da sabuwar gwamnati da majalisar dokokin tarayya, ta hanyar da ba ta dace ba.”

Ma'anar gwamnatin riƙon-ƙwarya

Gwamnatin riƙon-ƙwarya na nufin gwamnatin wucin-gadi ko kuma gwamnatin da ake kafawa na wani ɗan lokaci.

Wasu kuma kan kira ta gwamnatin miƙa mulki.

Ana kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ne don ta yi aiki kafin samar da zaɓaɓɓiyar gwamnati mai zuwa.

A mafi yawan lokuta babban aikinta shi ne tsara harkokin siyasa da kuma yadda za a yi zaɓe domin samar da sabuwar gwamnati.

Manyan masu riƙe da lamurran ƙasa ne ke zaɓen waɗanda za su jagoranci irin wannan gwamnati, mafi yawan lokuta a lokacin da aka kawo ƙarshen wani yaƙin basasa.

Haka kuma, ana kafa irin wannan gwamnati a duk lokacin da aka soke zaɓe a ƙasa mai bin tafarkin dimokraɗiyya, bayan cikar wa’adin gwamnati mai ci.

A Najeriya an kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙarshe ne shekaru 30 da suka gabata, a 1993, lokacin da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaɓen da aka gudanar, wanda aka yi wa laƙabi da June 12.