Ngolo Kante zai bar Al-Ittihad, Rabiot ya kusa komawa Man United

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na son siyar da Mason Mount, Adrien Rabiot zai iya komawa Old Trafford, Arsenal ta kusa daukar matashin golan nan Tommy Setford.

A shirye Manchester United take ta siyar da dan wasan tsakiyarta dan Ingila Mason Mount, mai shekara 25, a wannan bazarar. (HITC)

Dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 29, ya kusa kulla yarjejeniya da Manchester United bayan ya bar Juventus a karshen kwantiraginsa. (Goal)

Arsenal na shirin sayen golan Ingila Tommy Setford, mai shekara 18, daga Ajax, kafin rangadin da za su yi a Amurka. (Evening Standard)

Arsenal na kara kokari wajen sayen dan wasan bayan Italiya Riccardo Calafiori, mai shekara 22, daga Bologna. (The Athletic)

West Ham ta kulla yarjejeniyar baka da baka don siyan dan wasan tsakiyar Faransa N'Golo Kante, mai shekara 33, daga Al Ittihad. (The Athletic)

Aston Villa na shirin siyar da dan wasan bayan Faransa Lucas Digne, mai shekara 31. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 23, ya amince da yarjejeniyar sirri da Manchester United, wadda ke ci gaba da tattaunawa da Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)

Manchester United ta sanya farashin £30 kan dan wasan tsakiyar Scotland Scott McTominay mai shekaru 27. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Denmark Jesper Lindstrom, mai shekara 24, na shirin tafiya aro na tsawon kaka daya zuwa Everton daga Napoli. (CalcioMercato)

Brighton ta tattauna da Inter Miami kan cinikin dan wasan tsakiyar Paraguay Diego Gomez mai shekaru 21. (Sky Sports)

Birmingham City na sa ido kan dan wasan Fulham da Wales Luke Harris, mai shekara 19. (Football Insider)

Lille na neman sayen dan wasan bayan West Ham na Morocco Nayef Aguerd, mai shekara 28, a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan bayan Faransa Leny Yoro, mai shekara 18, wanda ya kulla yarjejeniya da Manchester United. (L'Equipe)

Chelsea na shirin sake tura dan wasan tsakiyar Brazil Andrey Santos, mai shekara 20, aro zuwa Strasbourg bayan kammala rangadin da suka yi a Amurka. (Fabrizio Romano)

Everton za ta yi kokarin dauko dan wasan Manchester City da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 28. (Football Insider)