Onana na dab da tafiya Aston Villa, Ingila za ta jira Guardiola ya bar Man City ta ɗauke shi

An wallafa

Matashin ɗan wasan tsakiya na Everton Amadou Onana na Belgium, mai shekara 22 na dab da kammala komawarsa Aston Villa zuwa ƙarshen makon nan. (Sky Sports)

Tsohon kociyan Liverpool Jurgen Klopp ba shi da sha'awar karbar aikin horad da tawagar Ingila. (Sky Germany)

A shirye hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila take ta jira Pep Guardiola ya bar Manchester City kafin ta naɗa shi a matsayin wanda zai maye gurbin Gareth Southgate a matsayin kociya na dindindin. (Independent)

Shi ma kociyan Tottenham Ange Postecoglou na daga cikin waɗanda ake sa ran zaɓa domin maye gurbin na Southgate. (Telegraph)

Fafutukar Al Nassr ta neman mai tsaron ragar Juventus Wojciech Szczesny na Poland, mai shekara 34 ta gamu da tazgaro. (Athletic )

Paris St-Germain ta ƙara dagewa a ƙoƙarin da take na ganin ta sayi ɗan gaban Napoli, Victor Osimhen na Najeriya, abin da zai iya kawo ƙarshen zawarcin ɗan Najeriyan da Chelsea ke yi. (Talksport)

Kusan Liverpool ta janye daga fafutukar sayen ɗan bayan Lille, wanda zai tafi Manchester United Leny Yoro, mai shekara 18, saboda alamu sun nuna yana sha'awar tafiya Real Madrid ne kawai. (Mirror)

Ƙungiyar Birmingham City na sha'awar matashin ɗan gaban Aston Villa Louie Barry, na Ingila. (Football Insider)

Har yanzu kuma Bayer Leverkusen na bin Villa sama da rabin kuɗin cinikin ɗan wasan gaba na gefe Moussa Diaby, na Faransa mai shekara 25, wanda ya kusa tafiya Al Ittihad ta Saudiyya. (Football Insider)

West Ham na samun nasara a ƙoƙarin sayen ɗan gaban Arsenal Reiss Nelson, mai shekara 24, ɗan Ingila da Gunners ta yi wa kuɗi fam miliyan 25. (Talksport)

Ɗan wasan gaba na gefe na Leeds Crysencio Summerville, mai shekara 22, ya tattauna da Chelsea, to amma kuma ƙungiyar Rennes ta Faransa, ita ma ta yi magana da ɗan Holland ɗin. (Teamtalk)

Huddersfield Town na tattaunawa domin sayen ɗan wasan tsakiya na Wolves Joe Hodge, mai shekara 21, bayan da ɗan wasan na tawagar Jamhuriyar Ireland ta ƴan ƙasa da shekara 21 ya shafe kakar da ta wuce a zaman aro a Queens Park Rangers. (Football Insider)

Barcelona ta gabatar da buƙatarta ga ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, a ƙoƙarin cimma yarjejeniya ta baki da ɗan Sifaniyan kafin wata ƙungiya ta Ingila ta neme shi. (Fabrizio Romano)

West Ham ta yi nisa a tattaunawar sayen ɗan bayan Manchester United. Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 26, (Teamtalk)