Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Plymouth ta naɗa Rooney sabon wanda zai horar da ita
Ƙungiyar dake buga Championship, Plymouth Argyle ta ɗauki tsohon ƙyaftin ɗin Ingila, Wayne Rooney a matakin sabon kociyanta.
Mai shekara 38 ya maye gurbin Ian Foster, wanda ta kora ranar 1 ga watan Afirilu, bayan da ƙungiyar ba ta taka rawar gani ba.
Wannan shi ne karon farko da Rooney zai horar da tamaula tun bayan da Birmingham City ta sallame shi ranar 2 ga watan Janairu.
Tsohon ɗan wasan Manchester United ya yi aiki kasa da wata uku da rashin nasara tara daga 15 da ya ja ragama a Birmingham.
Blues, wadda take buga karawar cike gurbi a Champions League lokacin da Rooney ya karbi ragama, ta koma gasar League One a farkon watan nan.
Wannan shi ne karo na hudu da Rooney ke karbar jan ragamar ƙungiya - wanda shi ne kan gaba a matakin wanda yafi ci wa Ingila ƙwallaye 53 daga baya Harry Kane ya sha gabansa a Maris ɗin 2023.
Ya horar da Derby County, wadda ta yi fama da matsin tattalin arziki.
Rooney ya ja ragamar Rams ta ci gaba da Championship a Mayun 2021 a kakarsa ta farko, amma ya bar ƙungiyar bayan da ta faɗi daga gasar, sakamakon kwashe mata maki 21, saboda matsin tattalin arziki.
Ya yi wata 15 a kociyan DC United ta Amurka, amma ya bar kungiyar cikin Oktoba, wanda ya karbi aiki Birmingham.
Zai gudanar da aikin tare da Kevin Nancekivell da Simon Ireland da mai horar da mai tsaron raga, Darryl Flahavan.