Man United ta kare a mataki mafi muni a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League, bayan da aka kammala wasannin 2023/04 ranar Lahadi.
United din ta je ta doke Brighton 2-0 a wasan mako na 38, inda Diogo Dalot ya fara cin ƙwallo daga baya Rasmus Hojlund ya kara na biyu.
Duk da nasarar da United ta samu ta kare a mataki na takwas a teburi - mataki mafi muni da ta kammala tun bayan 1989/90.
Haka kuma ƙungiyar ta yi rashin nasara tara a Old Trafford - karo biyu kenan da ta yi wannan rashin kokarin a tarihinta.
An kuma zura kwallo 58 a ragar United a Premier League ta bana, karon farko da aka zura mata kwallaye da yawa a gasar.
United ta kare kakar bana da rarar kwallo a raga a karon farko a tarihi, tun bayan 1989/90.
Ƙungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama, wadda ta buga wasa 38 ta ci karawa 18 da canjaras shida da rashin nasara 14 da cin ƙwallo 57 aka zura mata 58a raga da maki 60.
A bara ƙungiyar dake Old Trafford ta kare a mataki na ukun teburi da maki 75, wadda ta samu gurbin buga Champions League.
Sai dai United ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar ta zakarun Turai, wadda ta karkare a matakin karshe da maki hudu.
Bayern Munich ce ta yi ta daya a rukunin farko da maki 16, sai FC Kobenhavn ta biyu da maki takwas da kuma Galatasaray ta uku da maki biyar.
Haka kuma United mai rike da League Cup a bara ta yi rashin nasara a hannun Newcastle United da ci 3-0 ranar 1 ga watan Nuwambar 2023.
To sai dai United ta kai wasan karshe a FA Cup na bana, inda za ta buga wasan karshe da Manchester City ranar 25 ga watan Mayun 2024 a Wembley.
A bara City ta lashe FA Cup bayan da ta doke United a Wembley da ci 2-1.
Idan United ta yi nasarar lashe FA Cup za ta samu gurbin buga Europa League kai tsaye, yayin da











