Mazauna Shiroro a Najeriya na neman ƙarin ɗauki bayan 'harbo jirgin sojoji'

Asalin hoton, Getty Images
Mazauna yankin Shiroro na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya sun nemi gwamnatin tarayya ta ƙara yawan jami'an tsaro a yankin nasu bayan 'yan fashin daji sun harbo jirgin saman sojin ƙasar.
A ranar Litinin da yamma Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar jirginta ƙirar helikwafta ya yi hatsari a ƙauyen Chukuba yayin da yake aikin ceton mutanen da suka ji rauni.
Amma sanarwar da rundunar sojin ta fitar ba ta bayyana dalilin da ya jawo hatsarin ba, da mutanen da ke cikinsa, da kuma ko an samu rasa rai.
Wasu rahotanni sun ce jirgin ya je kai wa wasu sojoji agaji ne sakamakon hare-haren 'yan fashin daji da suka yi sanadiyar kashe dakarun na Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata majiya daga sojin Najeriya na cewa sojoji aƙalla 26 ne suka mutu a kwanton-ɓaunar da 'yan bindigar suka yi musu ranar Lahadi da dare tare da raunata wasu takwas.
Sai dai Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Akilu Isyaku Kuta, ya faɗa wa BBC Hausa cewa 'yan fashin daji ne suka harbo jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Kaduna.
"Abin da muka sani shi ne, jirgin ya je wucewa ne ta daidai inda ɓarayin suka yada zango, ba yaƙi ya je yi ba, wucewa zai yi zuwa Kaduna," in ji Akilu.
"A daidai wannan wajen ne suka harbe shi [jirgin]," kamar yadda ya bayyana.
Ita ma majiyar AFP ta tabbatar da hakan, tana mai cewa jirgin yana ɗauke da gawar sojoji 11 da kuma bakwai da aka jikkata lokacin da ya yi hatsarin.
Ya ƙara da cewa rahoton tsaro da ya samu ya bayyana cewa hari ne jirgin ya je ne domin duba abin da ya faru bayan harin da 'yan bindigar suka kai a Wushishi da ke maƙwabtaka da Shiroro.
Ƙananan hukumomin Shiroro da Wushishi na da nisan kilomita 75 daga Minna babban birnin jihar Neja.
'Yan fashin daji sun daɗe suna tafka ta'asa inda suke da sansanoni a dazukan da suka ratsa jihohin Neja da Zamfara da Katsina da Kaduna, dukkansu a arewacin Najeriya.
Masana harkokin tsaro na cewa har yanzu akwai wurare masu faɗi da babu jami'an tsaron Najeriya a wurin, abin da ya sa 'yan bindigar ke iko da su har ma suke saka wa mazauna yankunan haraji.
'Jami'an tsaro sun yi mana kaɗan'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Honarabul Akilu Isyaku Kuta ya ce zuwa lokacin da ya yi magana da BBC ba shi da cikakkun alƙaluman mutanen da suka mutu a hare-haren na Wushishi, kodayake dai ƙura ta lafa.
Rahotanni sun ce maharan sun far wa ƙauyukan ne tun a ranar Juma'a, abin da ya sa manoma da yawa suka gudu zuwa Wushishi da Zungero.
Sai dai honorabul ɗin ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar take yi, jami'an tsaro sun yi kaɗan a ƙaramar hukumarsa ta Shiroro.
"Muna da jami'an tsaro a wannan yankin amma ba su ishe mu ba," in ji shi. "Gwamnatin jiha na ƙaƙarin ganin an ƙaro su daga Abuja saboda muna da daji mai faɗi."
Ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da rahotonnin da ke cewa an kashe 'yan banga da dama a harin.
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ranar Talata ya ambato mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Janar Onyema Nwachukwu, na cewa hafsan sojin ƙasa Janar Taoreed Lagbaja na kan hanyarsa ta zuwa wurin da abin ya faru.
"Abin da muka saka a gaba yanzu shi ne rarrashin waɗanda [sojoji] suka mutu suka bari," a cewarsa, amma bai faɗi adadin sojojin da suka mutu ba.
Babu wasu alƙaluma da ke nuna yawan jami'an tsaron da ke ƙaramar hukumar ta Shiroro ko kuma jihar Neja baki ɗayanta.
A watan Nuwamban 2022, hafsan sojan ƙasa na Najeriya na lokacin, Janar Farouk Yahaya ya ƙaddamar da wani shirin soja da suka kira "Exercise Mugun Bugu" a jihar.
Ya ce aikin wani ɓangare ne na yaƙi da hare-haren 'yan fashi da masu iƙirarin jihadi a yankin arewa ta tsakiyar ƙasar.
Jirgin da aka harbo
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce jirgin nata ƙirar helikwafta ya yi hatsari a kan hanyarsa ta kai ɗauki a ranar Litinin da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ƙauyen Chukuba da ke jihar Neja.
Kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce jirgin mai lamba MI-171 ya tashi ne daga makarantar firamaren Zungeru da niyyar zuwa Kaduna amma daga baya aka gano ya yi hatsari a kusa da Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro.
Sanarwar ta ce ana can ana ci gaba da aikin ceto matuƙin jirgin da sauran fasinjojin da ke cikinsa, da kuma binciko musabbabin hatsarin.









