Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea na dab da daukar Caicedo, Everton za ta sabunta kwantiragin Alex Iwobi
Chelsea na dab da daukar dan tsakiyar Brighton Moises Caicedo, mai shekara 21, a kan kudi fam miliyan 115, a yayin da dan wasan dan kasar Ecuador ya gwammaci ya manta da Liverpool. (Sunday Telegraph - subscription required)
Liverpool ta shirya barwa Chelsea dan wasan Belgium Romeo Lavia, wanda yay a shirya barin Southampton a kan kudi fam miliyan 55. . (Mail)
Har wayau, mai kulub din Liverpool John Henry, zai halarci gasar firimiya League inda kungiyar ta sa da kuma Chelsea za su kece raini a Stamford Bridge. . (Sunday Mirror)
Mai tsaron ragar Denmark, Kasper Schmeichel, mai shekara 36, zai bar Chelsea inda zai koma Nice don maye gurbin dan wasan Spaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 28, wanda ya koma Real Madrid a kan aro. (Guardian)
Brighton na sha’awar Tyler Adams, na kungiyar Leeds bayan Chelsea ta janye daga yarjejeniya a kan dan wasan dan kasar Amurka da kuma ta dan kungiyar Ajax dan kasar ghana Mohammed Kudus, saboda suna son maye gurbinsu da Caicedo. (Independent)
Kocin Manchester City Pep Guardiola, ya mayar da daukar dan wasan West Ham Lucas Paqueta, babban abin da zai sanya gaba bayan Kevin de Bruyne, ya samu rauni a wasan da suka ci 3.0 a kan Burnley. (Talksport)
West Ham ta shirya taya dan wasan Montpellier, kuma dan gaban Faransa Elye Wahi, wanda kuma Chelsea da Eintracht Frankfurt ke harinsa. (L'Equipe - in French)
Tottenham za ta kafa tarihi wajen cinikin dan wasan da zai maye gurbin Harry Kane bayan ta syaar da shi ga kungiyar Bayern Munich. (Football Insider)
Har yanzu Everton na tattaunawa da dan tsakiyar Najeriya Alex Iwobi, mai shekara 27, a kan sabuwar kwantiragi a yayin da yake shekarar karshe ta kwantiraginsa da kungiyar. (Liverpool Echo)
Dan gaban Brazil Neymar, na dokin komawarsa Barcelona, a yayin da dan wasan mai shekara 31, ke neman barin Paris St-Germain. . (Sport - in Spanish)