Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern Munich ta kammala daukar Kane daga Tottenham
Harry Kane ya kammala komawa Bayern Munich kan yarjejeniyar kaka hudu, abin da ya kawo karshen zamansa a Tottenham a matakin wanda ke kan gaba a ci mata kwallaye.
Dan wasan ya koma Jamus kan kwantiragin fam miliyan 86.4, watakila ya buga Bayern German Cup da za ta kar da RB Leipzig ranar Asabar.
Kane ya bar buga Premier League a matakin wanda ya ci wa Tottenham kwallo 280 a wasa 435.
Wanda ke kan gaba a ci wa tawagar Ingila kwallaye a tarihi, ya yi atisaye a safiyar Asabar a shirin da Bayern ke yi na fuskantar RB Leipzig a German Cup ranar Asabar.
Tun farko an yi ta alakanta Kane da Manchester United a bana, daga baya Bayern Munich ta sanar da cewar tana zawarcin dan kwallon.
Kane ya lashe takalmin zinare karo uku a matakin wanda ci kwallaye da yawa a kakar Premier League, wato, Premier League Golden Boot.
Kane - wanda ya fara buga wa Tottenham tamaula a 2012 - ya zama kan gaba a cin kwallaye a Premier League a kakar 2015-16 da 2016-17 da kuma 2020-21.
Kyaftin din tawagar Ingila ya ci kwallo 213 a gasar Premier a wasa 320, saura 48 ya haura Alan Shearer, mai tarihin yawan cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Kane - wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Ingila kwallaye mai 58 - bai taba daukar wani babban kofi a Tottenham ko a Ingila ba.
Ita kuwa Bayern Munich kan dauki kofuna a kowacce kakar tamaula a Jamus, tana kuma daukar wasu a Turai.
Bayern Munich - wadda a yanzu Thomas Tuchel ke jagoranta - ta dauki Bundesliga na 33 jimilla, kuma a kakar da ta wuce ne ta dauki kofi na 11 a jere.
Zakarun na Jamus na da kofin Zakarun Turai na Champions League shida da kuma German Cup 20.