Gakpo na son komawa Man United, Tottenham da Liverpool na zawarcin Amrabat

An wallafa

Dan wasan PSV da Netherland winger Cody Gakpo, mai shekara 23, ya ce zai duba yiwuwar komawa Manchester United, sai dai ba bu wata magana da ta shiga tsakaninsa da kungiyar kan hakan. (NRC - in Dutch)

Tottenham da Liverpool na sha'awar dauko dan wasan tsakiya na Morocco Sofyan Amrabat, mai shekara 26, daga Fiorentina da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Janairu. (90min)

Watakil AC Milan ta bi sahun Barcelona a zawarcin dan wasan Arsenal kuma na tsakiyar Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 21, idan sun amince da sai da dan wasan Portugal winger Rafael Leao, mai shekara 23, a watan Janairu (Calciomercato - in Italian)

Ta yiwu Arsenal ta dage shirin dauko dan wasan Shakhtar Donetsk da Ukraine Mykhailo Mudryk, dan shekara 21, bayan raunin da dan wasan gaba na Brazil Gabriel Jesus ya ji masa. (Sun)

Dan wasan tsakiya na France Adrien Rabiot, mai shekara 27, ya ce zai so ya buga wasan Premier League. Kwantiragin dan wasan  zai kare a shekarar 2023. (Express)

Bayern Munich ta shirya tsaf domin yi wa dan wasan gaba na Jamus Jamal Musiala, mai shekara 19, ta yin sabon kwantiragi. (Bild - in German)

Manaja Eddie Howe ya ce batun kudi ka iya takawa Newcastle birki, wajen sayen 'yan wasa a watan Janairu. (Mail)

Roma sun fara tattaunawa da dan wasan gaba na Netherland Memphis Depay mai shekara 28, kan batun komawarsa kungiyar daga Barcelona(Sport - in Spanish)

Atletico Madrid a shirye ta ke ta bada dan wasan gaba na Portugal mai shekaru 23 Joao Felix, wanda ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar. (TVE, via Mail)

West Ham na son dauko sabon dan wasan mai kai hari a watan Janairun 2023, idan an bude kasuwar 'yan wasa. (Sun)

Manajan kungiyar kwallon kafar maza a Amurka, Gregg Berhalter zai tattauna da masu ruwa da tsaki saboda sayo sabbin 'yan wasa. (ESPN)