Messi da Benzema da Mbappe 'yan takarar gwarzon kwallon kafa na 2022

Fifa the Best

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fifa, ta bayyana Karim Benzema da Lionel Messi da Kyalin Mbappe cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2022.

Za a tuna Benzema kan kwallo 15 da ya ci a Champions League da ta kai Real Madrid ta lashe kofin na 13 jumulla.

Haka kuma tsohon dan kwallon tawagar Faransa shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a La Liga a ba.

Shi kuwa Mbappe, wanda PSG ta lashe Ligue 1 a bara ya ci kwallo 26 a wasa 46 da ya yi wa kungiyar Faransa.

Ya kuma taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar da lashe takalmin zinare da cin uku a wasan karshe da Argentina ta lashe kofin a bugun fenariti.

Messi kyaftin din Argentina ya taka rawar gani a Paris St Germain tun bayan da ya koma Faransa da taka leda daga Barcelona a 2021.

Ya bayar da gudunmuawar da PSG ta lashe Ligue 1 a kakar farko da ya buga mata tamaula.

Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin, shi aka bai wa fitatcen dan wasa a babbar gasar tamaula ta duniya ta 2022.

Za a karrama fitatcen dan wasan tamaula na duniya a bana, kan rawar da ya taka tsakanin 8 ga watan Agustan 2021 zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa a bikin da za a gudanar ranar 27 ga watan Fabrairun 2023.

An tace ukun daga 14 da aka bayyana a baya, inda aka sa wasu kwararru suka tankade su zuwa ukun karshe da za a fidda gwani.

Za kuma a gudanar da zaben tsakanin koci-koci na tawagar mambobin Fifa da kyaftin-kyaftin da wasu 'yan jarida da kuma kada kuri'a a yanar gizo ta Fifa.