Marubucin da wakokinsa suka hada kan al'ummar Somaliya

Somalia
Bayanan hoto, Mohamed Ibrahim Warsame
An wallafa

Daga Mary Harper Editar Afirka, BBC World Service News

Ana kallon al’ummar Somalia a matsayin "kasar marubuta wakokin baka" kuma babu wani mawaki da ya shahara a zamanin nan kamar Mohamed Ibrahim Warsame, wanda ya rasu a garin Hargeisa yana da shekara 79, a garin Hargeisa, inda ya kasance babban birnin Somaliland, da ya ayyana cin gashin kai.

Dubun dubatar mutane sun halarci jana'izarsa, yawancin mutanen sun niko gari tun daga kasashe makwabta kamar Habasha da Kenya da Djibouti, domin yin ban-kwana da fasihin marubucin.

Dandazon mutanen da suka taru a wurin jana'izar marigayin, da kabarinsa, sun zo domin addu’a da girmamawa ga Hadraawi, mai saukin kai, wanda jama’a ke kauna da kuma suke yi wa lakabi da "masanin kalamai", sunan da ake kiran sa da shi tun yana matashi a kasar Yemen, inda aka tura shi ya zauna tare da ‘yan uwa bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, ya ce: "Dukkan ‘yan Somalia na jimamin mutuwar Hadraawi."

Lokacin da na yi bincike na musamman kan rayuwarsa a shekarar 2017, kusan duk mutanen da na zanta da su, da zarar na tambaye su game da shi sai su fara rera wasu daga cikin baitukan da marigayin ya yi fice wajen rera su.

Mata ‘yan makaranta, da attajirai da mabarata da sojoji, da masu aikin sayar da abinci, kai har da ministocin gwamnatin Somalia sun haddace wakokin marigayin.

 

'Ya hada kawunanmu'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Wani abu da ya hada kawunan ‘yan Somalia, su ne wakokin Hadraawi," in ji Muhammad Suleiman, mataimaki kuma editan wasu daga cikin ayyukan da mawakin ya yi.

"Kawunan ‘yan Somalia sun rarrabu, kasar ta daidaice baki daya. Abu guda da ya ci gaba da sanya mu zama tsintsiya madaurinki daya shi ne harshenmu, da addininmu sai kuma wakokinsa."

Ba wai a fannin waka kadai Hadraawi ya yi fice ba. Yana rubuta wasan kwaikwayo na dandamali, yana aikin hadin gwiwa da mawakan Somalia, inda suka rera wakokin soyayya guda 70.

Ana yi masa kallo a matsayin masanin falsafa, mai karfafa gwiwar jama'a, ya taka muhimmiyar rawa wajen alkinta harshen Somalia a shekarar 1972.

Ya yi fice wajen sukar mulkin mulaka’un tsohon shugaban Somalia Siad Barre, da ya jagoranci kasar daga shekarar 1969 zuwa 1991.

A shekarar 1973 aka daure Hadraawi tsawon shekara biyar a gidan kaso, kan wata wakarsa da ya yi wa shugabannin Somalia shagube.

Wakar da ta yi matukar bata musu rai, musamman wakar Kashe Rakuma, da ke yaki da cin hanci da rashawa da mulkin danniya:

 

''Farin dokin ya saida ‘yancinsa

Kawai domin samun kyakkyawan diri.

Yayin da lamura irin haka ke faruwa

Dariya kanta na zama wani babban laifi

An shafe kasuwanci a kasarmu.''

 

Hadraawi mamba ne a kwamitin ‘yan tawayen Somalia na Somali National Movement, wanda nasarar da suka yi kan gwamnati ta kai Somaliland da ayyana ‘yancin kai a shekarar  1991, duk da cewa kasashen duniya ba su amince da ‘yancin ba, kuma ba sa kallon ta a matsayin kasa, face wani yanki na Somalia.

A shekarar 2003, ya yi kokarin kawo karshen tashin hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa a Somalia, wanda mawaka da ‘yan gambara da sauran kwararru kan al’adu suka taka rawa lokacin yakin yankin.

Ya yi kokarin tattauna batutuwan da suka shafi adalci, da sasanta kungiyoyi, har da kungiyoyin mata tsiraru, da iyaye mata da sauransu.

A shekarun da suka biyo baya, Hadraawi ya samu wani abin koyi da kwatance har da yi masa kallon wanda zai iya magance duk wata danbarwa ta hanyar amfani da kalamanshi masu saukin fahimta da dadin sauraro, ba a kasarsa kadai ba, har da duniya baki daya.

Wata mace na karanta littafin Hadraawi
Bayanan hoto, Hadraawi abin koyi ne ga 'yan Somalia

Marubucin wakar nan dan Scottland da aka yi wa lakabi da Farfesan rubuta wakoki a jami’ar Newcastle, Bill Herbert, ya yi aiki da fitattun malaman Somalia, inda suka fassara wasu daga cikin wakokin da Hadraawi ya rubuta, zuwa harshen Ingilishi.

"Yana da wata baiwa ta musamman, wata kwarewa, da fasahar yin magana ga mutane, da yadda mutanen ke saurarensa a nutse," in ji shi.

"Yana zabar kalmomi masu kaifi da shiga zukata da zarar an ambace su. Hadraawi yana da kaifin basira da hangen nesa kan tashe-tashen hankulan da Somalia ta samu kanta a ciki, da siyasar kasar, da halin jinkai da suke ciki, da kuma yanayin da rayuwa ta sauyawa ‘yan kasar."

 

'Ya bai wa mutane wurin zama'

 

Duk da cewa sukar gwamnati da fannin shari’a da yake yi ba tare da shakka ko tsoro ba, Hadraawi ya kasance kamili kuma mutumin kwarai. Murmushin da ke fuskarsa a ko da yaushe, na kara masa kyau da cikar zati.

Manajan daraktan hukumar raya al’adun Somalia  Kayd, kuma aminin Hadraawi, Ayan Mahamoud, ya ce:

"Yana da kyakkyawar zuciya, ana kiransa da suna 'geed' da harshen Somalia, ma’ana 'bishiya' saboda kamar yadda rassan bishiya ke taimakawa mutane samun inuwa da sauki daga rana, haka Hadraawi yake yi wa jama’a, kullum ba ya gajiya da taimakawa mutane da duk abin da ya mallaka ko da shi zai rasa."

 

Rubutattun wakokin Hadraawi, da yadda yake gabatar da suna bai wa mutane sha’awa da jan hankalinsu, ciki har da shugaban kamfanin Dahabshiil, Abdirashid Duale da suka yi fice kan harkar kasuwanci.

 

"Allah ya sanya min kaunar Hadraawi tun kafin na yi tozali shi," in ji shi.

 

"Wakokinsa sun koya min yadda zan yi mu’amala da mutane. Kafin na koma Birtaniya da zama, ya ba ni wata takarda dauke da wakar da ya rubuta, wadda ta yi bayanin yadda duniya take a wajen kusurwar Afirka wato inda muka fito.

Wakar ta koyar dani ilimin zaman duniya da zama da mutane ba tare da nuna bambanci ba. Shi ya ba ni kwarin gwiwar da na samu gina kasuwancina, wanda har yanzu a kan wannan turba nake."

Hadraawi ya yi fice ne ta fannin wakokin soyayya da ya rubuta, na siyasa. Wakarsa mai taken ‘’ soyayya da jini, na daya daga cikin fitattun da suka sanya ya kara fice da daukaka a duniyar wakoki:

 

''Ya ke masoyiyata

Farin ciki, kuma farin cikin zuciya.

A kan ki, zuciyata ta ginu da farin ciki

Tun daga lokacin da muka aminta da juna

Ke kadai ce abin da na damu da shi.''

 

Ficen da ‘yan Somalia suka yin a kaunar wakokin soyayya, na sanya su nishadi, babu tsoho babu yaro, kuma ba mace babu namiji, kowa na kaunar wakar soyayya.

Hadraawi ya sha halartar wuraren da akan shirya wasannin Gala, inda daruruwan mutane ke halarta, tare da ‘ya’yansu, idan ya na rera wakar haka za ka ga su na shilla yaran su sama suna cafkewa cikin nishadi.

Wadanda ke wajen dandalin da ba su samu shiga ba, kan dora ‘ya’yansu a kafada domin su hango gwaninsu,  Hadraawi baban soyayya.

Yadda mutane ke cika kamar taro nidi, ya sanya sai an sanya allon majigi a waje, saboda wadanda ke nesa sus amu kallo da sauraron kalamai masu dadi tamkar ana busa sarewa da ke fitowa daga bakin Hadraawi.

"Matasan Somalia sun shaida min wakokinsa sun koyar da su yadda za su tafiyr da komai na rayuywa," in ji Said Salah, wani farfesa da ya yi ritaya daga Jami’ar Minnesota a Amirka, wanda ya taba aikin rubuta wakokin Hadraawi guda uku a wasannin dandamali.

.

Mataimaki na musamman ga Hadraawi, Muhammad Suleiman, ya shafe shekaru masu yawa yana tattarawa da alkinta wakokin da mai gidansa ya rubuta har da jawabai da kasidu, wani aiki mai matukar wuya kasancewa Somalia na da al’adu da dabi’u masu saurin gaske.

"Hakika gangar jikin Hadraawi ta tafi. To amma, a gare mu har yanzu ya na raye tare da mu, saboda ayyukansa ba za su taba gushewa a doron kas aba, har abada har a tashi duniya."

Lokaci na karshe da na kasance da Hadraawi, alamu sun nuna ya san lokacin mutuwarsa na gabatowa. Kalaman karshe da ya fada min su ne: "daya bayan daya, waka ke bin wata wakar, kamar dai yadda rayuwa ta ke tafiya."