Yadda aka yi naɗin Sarkin Dutse Hameem Nuhu Muhammad Sunusi

An wallafa

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya miƙa sandar mulki ga sabon Sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi.

A wani ƙayataccen biki da ya gudana a filin taro na Aminu Kano da ke garin Dutse a ranar Asabar, dubban mutane sun halarci taro daga ciki da wajen jihar Jigawa domin dai taya sabon sarki murnar naɗin nasa.

Gwamna Badaru ya ce yana fatan sabon sarkin zai ɗora kan irin abubuwan bajintar da mahaifinsa marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya yi.

Ga dai yadda bikin ya kasance cikin hotuna:

BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Lokacin da aka gabato da sandar mulki wadda Alhaji Badaru ya damƙawa Sabon sarki
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru lokacin da yake miƙa sandar mulki ga sabon Sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Yayin da masu naɗi ke sanya al-ƙyabba ga sabon sarki
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Lokacin da Sabon Sarkin Hameem ke gabatar da jawabin godiya bayan naɗin da aka yi masa
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Tsohon gwamnan Borno kuma zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasar Najeriya da ke jiran gado Kashim Shettima
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da Shehun Borno Abubakar ibn Umar El-Kanemi
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli daga dama sai kuma Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar daga hagu a bikin sarautar Sabon sarkin Dutse
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III lokacin da yake bayani game da rashin da aka yi na tsohon sarkin Dutsen Marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Sarakuna tare da 'yan raikyarsu a zaune wajen bikin Sarauta
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Daga ko ina mutane ne suka halarci taron naɗin
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Wasu mahalarta bikin da ya gudana kenan ke miƙa gaisuwarsu ga sabon sarkin
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Sabon Sarki Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi
bbc

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Wasu mata da suka halarci naɗin sarautar suke miƙa gaisuwa ga sabon Sarkin
BBC

Asalin hoton, @bappancey.ng

Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka halarci taron daga ciki da wajen jihar Jigawa