Yadda aka yi naɗin Sarkin Dutse Hameem Nuhu Muhammad Sunusi

An wallafa

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru, ya miƙa sandar mulki ga sabon Sarkin Dutse Alhaji Hameem Nuhu Muhammad Sunusi.

A wani ƙayataccen biki da ya gudana a filin taro na Aminu Kano da ke garin Dutse a ranar Asabar, dubban mutane sun halarci taro daga ciki da wajen jihar Jigawa domin dai taya sabon sarki murnar naɗin nasa.

Gwamna Badaru ya ce yana fatan sabon sarkin zai ɗora kan irin abubuwan bajintar da mahaifinsa marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya yi.

Ga dai yadda bikin ya kasance cikin hotuna: