Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sir Bobby Charlton ya mutu yana da shekara 86
Tsohon zakakurin Manchester United, Sir Bobby Charlton, ya mutu yana da shekara 86.
Dan wasan ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya a 1966 da Ingila ta kartbi bakunci.
Charlton ya buga wa tawagar Ingila wasa 106 da cin kwallo 49 - ya dade a matsayin mafi bajinta a kasar kafin daga baya Rooney ya karba, sai kuma Harry Kane da ke rike da gurbin.
A shekara 17 da ya yi wa United tamaula, ya lashe kofin lik uku da European Cup da kuma FA Cup.
Iyalan Charlton sun sanar cewa ya mutu ne yana tsaka da bacci a kan gadonsa a sanyin safiyar Asabar.
A cikin watan Nuwambar 2020 aka bayar da sanarwar cewar Charlton ya kamu da cutar ciwon mantuwa.
United ta mika ta'aziyya ga iyalan Charlton da cewa "daya ne daga fitattun 'yan wasan kungiyar da ya bayar da gudunmuwar da ba za a manta da shi ba".