Man United ta amince za ta dauki Lisandro Martinez daga Ajax

An wallafa

Manchester United ta amince za ta sayi dan kwallon Argentina, mai tsaron baya, Lisandro Martinez daga Ajax kan fam miliyan 57.

Ana sa ran dan wasan mai shekara 24, zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar da cewar za a iya tsawaitata shekara daya.

Zai koma Old Trafford idan an auna koshin lafiyarsa, idan kuma ya samu takardar izinin taka leda a Burtaniya.

Cinikin Martinez na fam miliyan 57 ya hada har da tsarabe-tsaraben fam miliyan 8.5 da kuma fam miliyan 2.2 da za a biya tsohuwar kungiyarsa.

Ya buga wa Ajax wasa 120, tun bayan da ya koma Netherlands daga Defensa y Justicia ta Argentina kan fam miliyan 6.3 a 2019, ya kuma taka leda a Newell's Old Boys.

Martinez ya yi wa Argentina wasa bakwai tun bayan da ya fara yi mata tamaula a Maris din 2019.

Shi ne na uku da United za ta dauka a bana, bayan Tyrell Malacia daga Feyenoord da kuma Christian Eriksen, wanda yarjejeniyarsa ya kare a Brentford.

Kungiyar Old Trafford ta sanar cewar ''Ina cike da murnar sanar da kulla yarjejeniya da Ajax.

''Har yanzu cinikin ya dogara da idan an kammala auna koshin lafiyarsa da cike wasu takardu.

''Har yanzu mai tsaron bayan yana da kwantiragi da Ajax da zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2025, amma Ajax ta amince za ta sayar da dan wasan kan fam miliyan 57 ga kungiyar Ingila.''

Martinez ya taka leda karkashin Erik ten Hag a Ajax da lashe Eredivisie a kungiyar a 2021 zuwa 2022 da kuma daukar Dutch Cup a 2021.

Shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ba kamarsa a Ajax a kakar 2021-22.