Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa Ingila za ta naɗa sabon koci?
Ingila na neman sabon koci.
Bayan jagorantar wasanni 102, tsawon shekara takwas, Gareth Southgate ya yi murabus a matsayin kocin Ingila bayan kashin da ƙasar ta sha a hannun Sifaniya a gasar Euro 2024 wasan ƙarshe.
Za a tuna shi a matsayin wanda ya jagoranci Ingila wasan ƙarshe a gasar cin kofin Turai, da wasan dab da ƙarshe a gasar cin kofin duniya.
Wa zai gaje shi? Sashen wasanni na BBC ya duba waɗanda za su iya maye gurbinsa.
Lee Carsley
Lee Carsley zai iya kasancewa cikin lissafin hukumar ƙwallon Ingila ta FA kasancewar shi ne kocin tawagar ƙasar ƴan ƙasa da shekara 21.
Ya daɗe a FA kuma ya lashe wa ƙasar kofi na ƴan ƙasa da shekara 21. Zai iya zama kocin riƙon ƙwarya kafin bazara a sanar da sabon kocin ƙasar.
Southgate ya taɓa jagorantar tawagar ƴan ƙasa da shekara 21 tsakanin 2013 zuwa 2016 kafin zama babban kocin tawagar ƙasar.
Carsley, mai shekara 50, ya tattauna da hukumomin ƙwallon Jamhuriyyar Ireland domin zama kocin ƙasar a bara amma ya amince ya ci gaba da horar da tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21.
Pep Guardiola
Kocin Manchester City an daɗe ana alaƙanta shi da zama kocin wata ƙasa, kuma ba shi aikin horar da Ingila zai faranta ran ƴan ƙasar da dama.
Guadiola ya samu nasarori a matsayin kocin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, kuma ya lashe dukkanin abin da koci ke buri a matakin kocin Barcelona da Bayern Munich da Manchester City.
Sai shekarar 2025 ne kwantaragin Guardiola za ta ƙare a ƙungiyar Manchester City, amma bayan nan, ba za a cire tsammani ba, kodayake albashin da zai karɓa wani ƙalubale ne.
Eddie Howe
Shi ma wani koci ne ɗan Ingila da ke da farin jini.
Kocin na Newcastle an daɗe ana alaƙanta shi da zama kocin Ingila tun rawar ganin da ya yi a Bournemouth.
Ya kuma sake nuna kansa da bajintarsa a Newcastle - ya jagorance su zuwa Gasar Zakarun Turai a kakar 2023-24, kodayake ba su samu gurbi ba a kaka mai kamawa.
Kocin mai shekara 46 ya sanya hannu kan kwantaragi mai tsawo har zuwa 2027, amma da wahala ya yi watsi da tayin zama kocin Ingila idan har dama ta samu.
Jurgen Klopp
Ɗaya daga cikin manyan masu horar da ƴanwasa, wanda yanzu ba shi da aiki.
Idan hukumar FA ta yanke shawarar ɗauko wani daga waje, tabbas Klopp zai shiga jerin waɗanda za a duba.
Tsohon kocin Liverpool da wahala ya samu, kasancewar ya ajiye aikinsa a Anfield, kuma yanzu yana buƙatar hutu. Amma idan har FA na iya jira - Klopp na iya shiga lissafi.
Kocin mai shekara 57 ana hasashen zai karɓi aikin horarwa a Amurka da kuma hasashen zai karɓi aikin horar da Jamus a matsayin magajin Julian Nagelsmann, idan ya yi murabus.
Mauricio Pochettino
Wani babban koci wanda shi ma yanzu ba shi da aiki a wannan bazara.
Tsohon kocin Tottehnam da PSG da Chelsea an fi alaƙanta shi da Manchester United - kafin Erik ten Hag ya tsawaita kwangilar shi - amma zai iya sake karɓar aiki a Ingila.
Zai iya zama magajin Southgate, yana zama ne a London, kuma yadda yake son ƙwallon ƙafa a Ingila zai iya shiga lissafi.
Ana kuma tunanin Pochettino ba ya buƙatar tafiya hutu bayan barin Chelsea a Mayu.
Graham Potter
Tsohon kocin Brighton yana cikin waɗanda aka fi alaƙantawa kasancewar rawar ganin da ya yi a shekara uku a Brighton.
Ya fuskanci ƙalubale bayan sallamar shi da Chelsea ta yi kasa da wata bakwai a Afrilun 2023 amma yana cikin masu horar da ƴanwasan Ingila da ake mutuntawa a ƙasar.
Sai dai babu tabbas ko zai so ya yi aiki a matsayin mai horar da ƴanwasan ƙasar maimakon ƙungiya, domin ya taɓa yin watsi da tayin horar da tawagar Sweden a baya kafin tattauna batun zuwa Ajax da Leicester.
Amma ana ganin da wahala ya iya yin watsi da tayin aikin Ingila.
Thomas Tuchel
Ɗaya daga cikin manyan masu horar da ƴanwasa da ke neman aiki a wannan bazara.
Wanda ya taka rawar gani a Chelsea bayan taimaka wa ƙungiyar lashe kofin Zakarun Turai a 2021, ya ajiye aikinsa a Bayern Munich a kakar da ta gabata duk da lallashinsa ya ci gaba.
Tuchel, wanda ya taɓa horar da manyan ƙungiyoyi kamar Paris St-Germain da Borussia Dortmund, zai iya karɓar aikin horar da Ingila kuma ana tunanin zai yarda ya tattauna da Ingila domin maye gurbin Southgate.
An bayar da rahoton cewa saura ƙiris ya maye gurbin Erik ten Hag a Manchester United kafin su sasanta bayan nasarar lashe kofin FA.
Wakilin sashen wasanni na BBC Nizaar Kinsella ya ce : "majiyoyi kusa da Tuchel sun shaida min cewa yana sha'awar aikin."
"Amma ba ya da tabbas FA za ta tuntuɓe shi, kuma ana iya kallonsa a matsayin wani daga waje."
Sauran waɗanda za su iya shiga lissafi
Magoya bayan Ipswich ba za su so wannan labarin ba amma kocinsu Kieran McKenna yana yin rawar gani a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu horar da ƴanwasa a ƙasar.
Ba mamaki ba ne idan sunansa ya shiga cikin ƴantakarar kocin Ingila.
Tsohon kocin Ingila Frank Lampard ma na iya shiga lissafi kamar yadda wasu ke ambata, da shi da kocin Middlesbrough Michael Carrick, da na Celtic Brendan Rodgers da tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho.