Arsenal na daf da daukar Calafiori, PSG na son Osimhen

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

West Ham na neman dawo da Fikayo Tomori gasar Premier, Arsenal na dab da daukar Riccardo Calafiori, Aston Villa ta shirya barin Matty Cash.

West Ham na sha'awar daukar dan wasan bayan AC Milan Fikayo Tomori, mai shekara 26. (Mail)

Arsenal na gab da kulla yarjejeniya da Bologna kan kudi fan miliyan 42.1 kan dan wasan bayan Italiya Riccardo Calafiori, mai shekara 22. (Sky Sports)

Aston Villa a shirye take ta siyar da dan wasan bayan Poland Matty Cash mai shekara 26 a wannan bazarar. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Manchester City dan kasar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33, bai cimma matsaya da kulob din Al Ittihad na Saudi Arabiya ba duk da rahotanni. (Talksport)

Manchester United ta yanke shawarar fasa sayen dan wasan tsakiya na Morroco Sofyan Amrabat, mai shekara 27, kan yarjejeniyar dindindin. (Tuttomercato)

Kulob din na Premier yana sha'awar ci gaba da rike Amrabat a kulob din bayan zmaan aronsa ya kare a kakar wasan da ta wuce, amma suna son tattaunawa ne kan sabon kwanatragi (Metro)

Ana sa ran dan wasan gaban Aston Villa na Faransa Moussa Diaby, mai shekara 25, zai kammala komawa Al Ittihad mako mai zuwa. (Talksport)

Villa za ta nemi maye gurbin Diaby da dan wasan gaban Atletico Madrid na Portugal Joao Felix mai shekaru 24. (Sun)

Shugaban Bayern Munich Uli Hoeness ya ce dan wasan bayan Holland Matthijs De Ligt, mai shekara 24, wanda Manchester United ke nema, zai iya barin kungiyar a kakar wasa ta bana. (Sky Germany)

United ba ta son barin dan wasan tsakiyar Scotland Scott McTominay, mai shekara 27, ya bar Old Trafford, sakamakon zawarcin Fulham da Tottenham. (Standard)

Paris St-Germain na shirin ci gaba da zawarcin dan wasan gaban Napoli na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 25. (Fabrizio Romano)

Kazalika PSG na son dauko dan wasan gefe na Napoli na Georgia Khvicha Kvaratshkelia, mai shekara 23, da kuma dan wasan tsakiya na Faransa mai shekaru 19 Desire Doue daga Rennes. (Sky Sports)