Indiya ta haramta sana'ar achaɓa a birnin Delhi

Mai sana'ar kabu-kabu a birnin Delhi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ƙasar Indiya ta haramta sana'ar achaɓa ko kabu-kabu a titunan Delhi, babban birnin ƙasar, lamarin da zai kawo nakasu ga kamfanonin da ke samar da baburan irin su Uber da Ola da kuma Rapido.

A wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce amfani da babur wajen ɗaukar fasinjoji ya saɓa wa dokokin ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a iya cin ''waɗanda suka saɓa dokar'' tarar kuɗi har zuwa rupee 100,000 kwatankwacin dala 1,206.70 ko sama da naira dubu 600.

Kawo yanzu dai kamfanonin da ke samar da baburan ba su ce komai ba.

Dubban mutane ne ke amfani da baburan masu sauƙi, domin gunadar da al'amuransu na yau da kullum a birnin mai cunkoson ababen hawa.

Haka kuma sana'a ce da ke samar wa dubban mutane ayyukan yi a ƙasar, inda wasu daga cikinsu ke amfani da baburansu na hawa wajen jigilar fasinjoji.

Amma a tsarin dokar ababen hawa ta Indiya, laifi ne yin amfani da abin hawa na ƙashin kai domin ɗaukar fasinjoiji.

Jaridar Indian Express ta zanta da wasu daga cikin 'yan achabar da haramcin ya shafa a birnin Delhi, waɗanda suka ce za su sha wahala wajen gudanar da rayuwarsu, kasancewar suna amfani da sana'ar ne wajen samun ƙarin kuɗi.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da sana'ar ke samun kanta cikin ruɗani a ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Janairu, gwamnatin jihar Maharashtra ta ƙi bayar da lasisi ga kamfanonin baburan haya na Rapido, tana mai cewa babu wata doka da ta goyi bayan ba su lasisin.

Babbar kotun Bombay ta umarci kamfanin ya dakatar da ayyukansa sakamakon rashin lasisi.

Daga nan kuma Kamfanin na Rapido ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙolin ƙasar, wadda ta tabbatar da hukuncin babbar kotun.

Wasu ma'aikatan wucin-gadi sun gudanar da zanga-zangar adawa da masu sana'ar ta kabu-kabu.

A cikin watan Disamban bara ƙungiyar ma'aikatan wucin-gadi a jihar Telangana ta rubuta wa gwamnatin jihar ƙorafinsu.

Ƙungiyar ma'aikatan wuci-gadin na neman hukumomin jihar da su ɗauki matakai kan masu amfani da baburansu na ƙashin kai wajen gudanar da sana'ar achaɓan.

Wani rahoton bincike da gamayyar ƙungiyar 'yan kasuwa da aka wallafa a shekarar da ta gabata ya nuna cewa kuɗin da sana'ar kabu-kabu a ƙasar ke samarwa ya kai dala miliyan 50, kuma ana sa ran zai iya ƙaruwa zuwa kusan dala biliyan 1.5 zuwa shekarar 2030.

To sai dai rahoton ya yi gargaɗin cewar dokokin shari'a da suka jiɓanci sana'ar, da kuma kafewar al'umma kan amfani da tsohuwar hanyar zirga-zirgar ka iya kawo cikas ga bunƙasar sana'ar.