BBC ta gano ƙungiyar maƙiya Musulunci da ke cikin masu aikin raba abinci a Gaza

- Marubuci, Andy Verity, Tom Beal & Will Dahlgreen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Kamfanin da aka bai wa kwangilar gadin wuraren raba abinci a Zirin Gaza na amfani da mambobin wata ƙungiya da aka sani da ƙiyayyar addinin Musulunci, kamar yadda wani binciken BBC ya gano.
BBC ta gano 10 daga cikin 'yan ƙungiyar da ke kiran kansu Infidels Motorcycle Club da ke aiki a Gaza ƙarƙashin kamfanin UG Solutions - wani kamfani da ke samar da tsaro a wuraren rarraba abinci na ƙungiyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF).
Ɗaruruwan Falasɗinawa aka kashe a wuraren raba abincin da ke da cike da hatsaniya da tashin hankali.
Mun gano cewa bakwai daga cikin gungun na riƙe da manyan muƙamai da ke sa ido a wuraren ƙungiyar da Amurka da Isra'ila ke ɗaukar nauyi.
UG Solutions (UGS) ya kare ma'aikatansa game da ayyukan da suke yi, yana mai cewa "babu ruwansa da abubuwan da ba su shafi aiki ba" na mutanen.
GHF ta ce ba ta taɓa yarda da "duk wasu ayyukan ƙiyayya, ko na wariya".
Tsofaffin sojin Amurka da suka yi yaƙi a Iraƙi a 2006 ne suka kafa ƙungiyar Infidels MC, waɗanda ke kallon kansu a matsayin mayaƙan 'yancin Kiristanci wato Crusaders na zamanin yanzu - kamar Kiristocin da suka yaƙi Musulmai wajen ƙwace iko da Birnin Ƙudus.
Gungun na ci gaba da yaɗa kalaman ƙiyayya ga Musulunci a shafukansu na Facebook, har ma suka taɓa shirya bikin babbaka alade a watan Ramadana mai tsarki domin nuna "rashin biyayya" ga Musulunci.
"Bai wa gungun Infidels MC gadin wurin raba abinci a Gaza tamkar bai wa KKK alhakin raba abinci a Sudan ne. Ba shi da wata ma'ana gaba ɗaya," a cewar Edward Ahmed Mitchell, mataimakin shugaban cibiyar Council on American-Islamic Relations (CAIR), wata ƙungiyar kare haƙƙin Musulumi a Amurka.
"Tashin hankali kawai zai jawo, kuma abin da muka dinga gani kenan a Gaza."
Shugaban gungun, Johnny "Taz" Mulford, tsohon saja ne a rundunar sojin Amurka da aka taɓa hukuntawa kan haɗa baki wajen bayar da cin hanci, da sata, da yin ƙarya ga mahukuntan soja. Yanzu shi ne "shugaban UG Solutions a Gaza" da ke kula da aikin kwangilar.

Asalin hoton, Facebook
Mun tura wa Infidels MC saƙon imel domin jin ta bakinsu. A martaninsu, Mista Mulford ya umarci mambobin ƙungiyar da kada su bayar da amsa amma kuma ya saka adireshin BBC cikin umarnin da ya aika wa kowa ta hanyar danna "reply all" kuma bisa rashin sani ya bayyana imel da sunayen abokan aikinsa, waɗanda wasunsu ke aiki a Gazan.
Bayan haɗa sunayensu da kuma bayanan da suke a fili game da Infidels MC, da kuma hujjoji daga wasu ma'aikatan UG Solutions, mun gano 10 daga cikin mambobin Infidels MC waɗanda Mulford ya ɗauka domin taya shi aiki a Gaza.
Bayan Mulford, mun kuma gano wasu manyan mambobi uku da ke da manyan muƙamai a wurin aikin UG na Gaza:
- Larry "J-Rod" Jarrett, wanda ake kira mataimakin shugaban Infidels MC, kuma shi ne mai kula da ayyuka
- Ma'aji na ƙasa, Bill "Saint" Siebe, wanda ke jagorantar tsaron ɗaya cikin huɗu na wuraren raba abincin GHF
- Richard "A-Tracker" Lofton, ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa gungun kuma shi ne shugaba a ɗaya daga cikin wuraren

Asalin hoton, Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sauran bayanai sun taimaka mana wajen gano sauran mambobi shida da aka ɗauka aiki a Gaza. Uku daga ciki masu riƙe da muƙamai ne.
Jarrett, da Siebe, da Lofton ba su bayar da amsar da BBC ta nema daga wajensu ba.
UGS ya faɗa wa BBC cewa yana gudanar da cikakken bincike kan mutane sannan kuma sai waɗanda ya tantance yake turawa fagen daga.
Sai dai kuma rahotonni sun nuna cewa shekara biyu da ta wuce an kama Mista Jarret a Amurka bisa yin tuƙi cikin maye, kuma an taɓa cin tararsa kan hakan shekara 10 da ta wuce. Babu tabbas ko an taɓa gurfanar da shi a gaban kotu.
An taɓa kama mamallaki kuma shugaban UG Soutions, Jameson Govoni, a farkon shekarar nan a North Carolina bisa zargin hannunsa a wani harin da aka bige wani da abin hawa, da kuma guje wa 'yansanda.
Govoni mazaunin Amurka ne amma ba mamban Infidels MC ba ne, kuma ya ƙi yarda ya ce uffan.
Cikin wani saƙo a dandalin sada zumunta a watan Mayu, Mista Mulford ya nemi tsofaffin sojan Amurka su aika masa saƙon neman aiki ta Facebook.

Jimilla, aƙalla mutum 40 ne cikin kusan 240 aka ɗauka domin yi wa UG Solutions aiki a Gaza daga gungun Infidels MC, a cewar ƙiyasin da wani tsohon ɗankwangila ya yi.
UG Solutions na biyan kowane ɗankwangila dala 980 a kullum, inda shugabanni kan samu har zuwa 1,580 a wuraren raba abinci na GHF, kamar yadda wasu takardu da BBC ta gani suka nuna.

Asalin hoton, Facebook
Kamfaninsa ya wallafa wani bidiyo a intanet da ke nuna harbe-harbe da bindiga, da kuma kashe miyagu ɗauke da saƙon: "Kada ku manta, ku yi ta harbi har sai sun daina yi muku barazana!"
Wani saƙo Infidels MC ya wallafa a Facebook na tallan hulunan "1095", na nuna lokacin da aka ƙaddamar da harin Crusades, "wani harin soja da dakarun Turawan Yamma suka kai domin ƙwace Birnin Ƙudus da Ƙasa mai Tsarki daga hannun Musulmi". Ƙasa mai Tsarki na nufin Isra'ila da yankunan Falasɗinawa a yanzu.

Asalin hoton, Facebook
"Idan kuka ga masu ƙyamar Musulunci na murnar harin 1095 na Crusade, suna murna ne kan kisan gillar da aka yi wa Musulmi - lokacin da aka karkashe Musulmi da Yahudawa a Birnin Ƙudus," in ji Mista Mitchell na ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi CAIR.
Ya ce gungun mutanen na da alamomin ƙiyayyar Musulmi da ke amfani da sunan "Infidels".

Asalin hoton, Facebook
Cikin abubuwan ƙiyayyar Musulunci da ƙungiyar ke yi har da shirya bikin babbaka alade yayin watan Ramadana, wanda BBC ta gani cikin wani shafin intanet da aka daina amfani da shi.
Saƙon na cewa: "Saboda saɓa wa koyarwar Musulunci a watan Ramadana mai tsarki... Infidels MC Colorado na gayyatarku wajen wani bikin cin naman alade da kuma yawo a kan babura."
Akwai kuma wani allon sanarwa da ke nuna wata mace sanye da doguwar riga ta abaya, wadda aka yaga ta daga tsakiya kuma take nuna ƙirjinta.
Shafin Facebook na Infidels MC cike yake da tattaunawar da ke nuna ƙiyayya ga Musulunci da Musulami, waɗanda ke kan shafin har zuwa ranar Laraba.

Asalin hoton, Internet Archive
An sha ganin tashin hankali da kashe-kashe a wuraren raba abinci na ƙungiyar GHF tun da suka fara aiki a Gaza a ƙarshen watan Mayu.
Zuwa 2 ga watan Satumba, an kashe yara da mata da maza 1,135 a kusa da wuraren raba abincin na GHF, a cewar alƙaluman ofishin ayyukan agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sojojin Isra'ila ne suka aikata kashe-kashen yayin da mutanen ke kan layin karɓar abinci.
Isra'ilar ta ce tana duba rahotonnin kashe fararen hula a wurin karɓar abinci.
Infidels MC ta ce tana da rassa 15 a Amurka da kuma reshe ɗaya a Jamus

Asalin hoton, Getty Images











