Champions League: PSG ta samu dama a kan Aston Villa

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paris St Germain ta doke Aston Villa 3-1 a wasan farko zagayen kwata fainal da suka kara ranar Laraba a Faransa.

Aston Villa ce ta fara zura na farko ta hannun Rogers, daga baya PSG ta farke ta hannun Doue.

Bayan da suka huta suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu, PSG ta kara na biyu ta hannun Kvaratskhelia, sannan Nuno Mendes ya kara na uku daf da tashi.

PSG, wadda tuni ta lashe Ligue 1 na bana, ta fuskanci Aston Villa a karon farko a gasar zakarun Turai a tarihi.

A kakar nan PSG ta doke Manchester City 4-2 a Champions League ranar 22 ga watan Janairu, ita ce ta fitar da Liverpool a gasar bana a zagaye na biyu, yanzu ta ci Aston Villa.

Karo na hudu kenan da ake cin kungiyar Premier League uku a Champions League a kaka ɗaya, bayan bajintar Bayern Munich a 2013/14 da Barcelona a 2018/19 da kuma Real Madrid a 2021/22.

Ranar Talata 15 ga watan Afirilu, Aston Villa za ta karɓi bakuncin wasa na biyu a Villa Park, wasan neman kai wa daf da karshe a Champions League.