Ƴan wasa ne kaɗai za su iya kawo sauyin da ake buƙata - Guardiola

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ƴan wasa ne kaɗai sa zu iya jagorantar duk wasu sauye-sauyen da ake buƙata game da yawan wasannin da ake bugawa a kowace kaka.
Ɗan wasan tsakiya na City da Sifaniya, Rodri, mai shekara 28, ya faɗa a ranar Talata cewa ƴan wasan ƙwallon ƙafa na dab da shiga yajin aiki domin nuna adawa da yawan wasannin da ake bugwa.
"Idan wani abu zai sauya, dole ne ya taso daga ɓangaren ƴan wasa, su ne kawai za su iya kawo sauyi," in ji Guardiola.
"Harkar ƙwallon ƙafa na iya gudana ba tare da masu horaswa ba da daraktocin wasanni da kafofin watsa labarai da masu mallakar ƙungiyoyi amma babu abin da zai iya faruwa ba tare da ƴan wasa ba, idan babu su, ba za ku iya wasa ba, su kaɗai ke da ikon yin hakan."
A watan Yuli, ƙungiyar ƴan wasan ƙwallon ƙafa ta duniya ta Fifpro ta ce za ta ɗauki matakin shari'a kan Fifa saboda abin da ƙungiyar ta kira "cin zarafi" a fagen ƙwallon ƙafa.
Wani rahoto da Fifpro ta fitar ya ce bai kamata ɗan wasa ya bugawa wasannin da suka wuce 50 zuwa 60 ba a kowace kaka, amma hakan ya danganta da shekarun ɗan wasa.
Kocin Chelsea Enzo Maresca ya yi na'am da kalaman Guardiola kuma ya amince cewa "babu shakka" akwai wasanni da yawa a kan jadawalin kowace shekara.
"Ba na jin muna kula da lafiyar ƴan wasan. Ba daidai ba ne adadin wasannin da ke akwai ba," in ji Maresca.










