Barcelona ta ce Gundogan ya je ya gwada sa'a a wata ƙungiyar

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta amince Ilkay Gundogan ya je wata ƙungiyar ya gwada sa'a a kakar nan da zarar ya samu dama.
Mai shekara 33 ya yi kaka ɗaya a Barcelona, bayan da ya bar Manchester City a lokacin da yarjejeniyarsa ya kare da ƙungiyar Etihad.
Duk da saura ƙwantiragin wata 12 ta rage masa a Barcelona, amma ta ce ta yadda ya koma wata ƙungiyar a bana da zarar ya samu dama.
Ana hasashen cewar ƙungiyoyin Premier League na son ɗaukar ɗan wasan, wanda ya buga wasa 15 a gabaki ɗayan kakar bara, inda Barcelona ta yi ta biyu a La Liga.
Kociyan Barcelona, Hansi Flick ya fayyace dalilin da Gundogan bai buga wasan La Liga ba ranar Asabar da suka doke Valencia 2-1.
Flick, wanda ya horar da Gundogan a tawagar Jamus ya ce zai so ci gaba da aiki tare da ɗan wasan, amma halin da Barcelona ta tsinci kanta na matsin tattalin arziki ya zama dole su barshi ya kara gaba.
An ce har yanzu ta kasa kulla yarjejeniya da Dani Olmo kan £51m, saboda kada ta karya dokar La Liga ta kashe ƙudi daidai samu.
Haka kuma ƙungiyar ta ce tana fatan cefanar da Vitor Roque kafin a rufu kasuwar cinikin ƴan kwallon Turai ta bana.
Tuni Barcelona ta sanar cewar kyaftin ɗinta, Sergi Roberto ya bar ƙungiyar, sannan Bournemouth ta kammala ɗaukar Julian Araujo a makon jiya.










