UEFA ta fara bincike kan raflin Premier da aka dakatar

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar alƙalan wasa ta PGMOL ta ce tana ɗaukar sabbin zarge-zargen da ake yi wa rafalin gasar Premier David Coote da 'matuƙar muhimmanci.'
An dakatar da Coote daga aikinsa har sai an gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya fito a farkon wannan makon, inda alƙalin wasan mai shekaru 42 ya furta ƙalaman ɓatanci kan tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp.
Hukumar ƙwallon ƙafar Turai Uefa ma ta ƙaddamar da nata binciken tare da dakatar da Coote.
A ranar Laraba, jaridar Sun ta buga hotuna da ta ce an ɗauka a lokacin gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, inda ake zargin cewa sun nuna Coote yana shakar wata farar hoda da naɗaɗɗiyar takardan kuɗin Amurka.
Coote ya yi aiki a a matsayin jami'in wasanni a lokacin gasar.
Jaridar The Sun ta ce Coote ya aika hotunan ne ga abokinsa a lokacin gasar.
Ya zuwa yanzu dai BBC ba ta iya tabntance sahihancin hotunan ko bidiyon ba, ta dai tuntubi Coote don jin ta bakinsa amma ya zuwa yanzu bai yi wani martani ba.






