Rodri na fatan dawowa wasa kafin ƙarshen kaka

A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wasa na uku na wannan kakar ne Rodri ya ji rauni a gwiwarsa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan tsakiyar Manchester City Rodri na fatan dawowa kwallo kafin arshen wannan kakar da muke ciki.

Rodri ya samu karaya ne a ƙafarsa ta dama a wasan da City da yi 2-2 da Arsenal a watan Satumba, raunin da kocin ungiyar Pep Guardiola ya ce zai iya jinya ta sauran lokacin kaka.

Da rashin Rodri, City ta yi rashin nasara a wasa shida a duka gasar da ta buga, yayin da ɗan wasan Spain ɗin ke fatan taimakawa ƙungiyarsa gabanin ƙarshen kakar wasanni.

"Burina shi ne na dawo gabanin ƙarshen wannan kakar. Ban yanke ƙauna ba a wannan kakar, amma ba na son yin kowanne irin kuskure. Tunanina shi ne jinyar watanni shida ko bakwai," kamar yadda Rodri ya shaida wa wata kafar labarai.

"Ina samun sauƙi sama da yadda na yi tsammani. Ina jin daɗin hutun da nake yi, idan har zan iya fadin hakan.

"Yadda nake ji kamar ba karye wa na yi ba, gwiwata na samun sauki. Ina da fatan babu wani tashin hankali.

"Idan ana maganar raɗaɗi, na sha wuya a wata ɗaya da rabin farko, bana iya tafiya, amma yanzu da sauƙi."

Za a kammala gasar Premier a ranar 25 ga watan Mayu, kwana takwas bayan an kammala wasan ƙarshe na FA a ranar 17 ga watan na Mayu.

City za ta buga wasanta na gaba da Liverpool a ranar Lahadi 1 ga watan Disamba a wasan mako na 13.