Haaland ya sabunta kwantiraginsa a Man City zuwa 2034

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaban ƙungiyar Manchester City ta Ingila, Erling Haaland ya sabunta kwantiraginsa domin cigaba da taka leda a ƙungiyar har zuwa shekarar 2034.
Haaland ya koma ƙungiyar ne daga Dortmund a shekarar 2022, kuma zuwa yanzu ya zura ƙwallo 111 a wasa 126 da ya buga, sannan ya lashe kofin Premier biyu da na FA Cup da na Champions League da kofin Super Cup.
Sabon kwantiragin na shekara tara da wata biyar na nufin ɗanwasan mai shekara mai shekara 24 zai cigaba da murza ƙwallo a ƙungiyar har sai ya kai shekara 34.
"Ina farin cikin sabunta kwantiragin da na yi, kuma ina farin cikin cigaba da kasancewa a wannan ƙungiya.
"Manchester City ƙungiya ce ta daban, wadda ke ƙunshe da mutane masu daraja, da magoya baya masu matuƙar ƙaunarmu," in ji shi, sannan ya ƙara da godiya ga kocinsa, Pep Guaediola.
Kimanin wata biyu da suka gabata ne shi ma kocin ƙungiyar, Guardiola ya sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar.
Wannan ne kwantiragi a gasar Premier League mafi tsayi, inda ya doke kwantiragin Cole Palmer, wanda shi ma ya shiga kwantiragi da ƙungiyar Chelsea na shekara tara a watan Agustan bara.








