Camavinga ya ji rauni ba zai buga Uefa Super Cup ba

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Real Madrid, Eduardo Camavinga ba zai buga Uefa Super Cup ba ranar Laraba a karawa da Atalanta, sakamakon raunin da ya ji.
Ɗan kasar Faransa, ya gurɗa gwiwa a lokacin atisaye a Warsaw a National Stadium ranar Talata.
Mai shekara 21 ya kuma ji raunin lokacin da ya yi karo da takwaransa ɗan kasar Faransa, Aurelien Tchouameni.
Tuni kuma likitoci suka auna girman raunin da ya ji, inda Real Madrid ta sanar da cewar a kafarsa ta hagun ya ji ciwon.
To sai dai ƙungiyar ba ta fayyace lokacin da zai kammala jinya ya koma fagen daga ba, amma ana jin zai kai mako bakwai.
Ya buga wa Real Madrid wasa 46 a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce, inda ƙungiyar ta lashe La Liga da Champions League.
Real Madrid za ta kece raini da wadda ta lashe Europa League a bara, Atalanta a Poland don cin Super Cup, inda Kylian Mbappe ake sa ran zai buga karawar, wanda ta ɗauka a bana daga Paris St-Germain.
Real Madrid za ta fara karawa a makon farko a gasar La Liga ta 2024/25 da Mallorca a Santiago Bernabeu ranar 18 ga watan Agusta.









