Flick ya ci Real Madrid karo huɗu a jere a kakarsa ta farko a Barca

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta doke Real Madrid 4-3 a wasan mako na 35 a La Liga da suka fafata ranar Lahadi a Estadi Olimpic Lluis Companys.
Barcelona ta ci ƙwallayen ta hannun Eric Garcia da Lamine Yamal da Raphinha da ya zura biyu a raga.
Ita kuwa Real Madrid, mai riƙe da La Liga na bata ta zura ƙwallayenta uku ta hannun Kylian Mbappe ta farko a bugun fenariti.
Wasannin da aka buga tsakanin Barca da Real a kakar nan:
Kakar 2024/2025
Spanish La Liga ranar Lahadi 11 ga watan Mayun 2025
- Barcelona 4 - 3 Real Madrid
Copa del Rey ranar Asabar 26 ga watan Afirilun 2025
- Barcelona 3 - 2 Real Madrid
Spanish Super Cup ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025
- Real Madrid 2 - 5 Barcelona
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Spanish La Liga ranar Asabar 26 ga watan Oktoban 2024
- Real Madrid 0 - 4 Barcelona
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama a mataki na ɗaya a kan teburi da maki 82, Real tana mataki na biyu da maki 75.
Haka kuma Kylian Mbappe ya zama kan gaba a yawan cin ƙwallaye a La Liga mai 27 a raga, Robert Lewandowski na Barcelona mai 25 a raga ya koma mataki na biyu.
Sauran wasannin da suka rage a gaban Barcelona a bana:
Spanish La Liga ranar Alhamis 15 ga watan Mayu
- Espanyol da Barcelona
Spanish La Liga Su 18May 2025
- Barcelona da Villarreal
Spanish La Liga Su 25May 2025
- Ath Bilbao da Barcelona
Sauran wasannin da suka rage a gaban Real Madrid a kakar nan:
Spanish La Liga ranar Laraba 14 ga watan Mayu
- Real Madrid da Mallorca
Spanish La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Mayu
- Sevilla da Real Madrid
Spanish La Liga ranar Lahadi 25 ga wwatan Mayu
- Real Madrid da Sociedad
Tuni dai Barcelona ta lashe kofi biyu a kakar nan, wato Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey, kuma a kan Real Madrid a wasan na hamayya na El Clasico.
Kawo yanzu Barcelona ta ci ƙwallo 95 a La Liga a bana a wasa 35, karon farko a wannan ƙwazon tun bayan 2016/17 da ta ci ƙwallo 101.
Kociyan Real Madrid ya yi rashin nasara 13 daga wasa 26 da ya ja ragamar El Clasico, ya ci 10 da canjaras uku.
Shi kuwa mai horar da Barcelona, Hansi Flick ya ci El Clasico huɗu a dukkan fafatawar da suka yi a bana.
Har yanzu Pep Guardiola ne kan gaba a yawan nasara a El Clasico a kakarsa ta farko da ya doke Real Madrid sau biyar tsakanin 2008 zuwa 2010.
Ƴan Barca da suka fuskanci Real Madrid:
Hansi Flick ya kara fitar da ƴan wasan da ya fuskanci Inter Milan da su a karawa ta biyu a Champions League ranar Talata, inda Inter ta kai zagayen karshe.
Barcelona ƴan wasa 11: Szczesny, Martín, Martínez, Cubarsí, García, Olmo, De Jong, Pedri, Raphinha, Ferran Torres, Yamal.
Ƴan benci: Ter Stegen, Balde, Araujo, Gavi, Lewandowski, Fati, Pena, Christensen, Fermin, Casado, Pau Victor, Fort.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Real da suka fafata da Barcelona:
Real Madrid ba ta sauya ƴan wasan da ta fuskanci Celta Vigo da su ba a wasan da ta ci 3-2 a La Liga a makon jiya - Kylian Mbappe ne ya ci biyu a karawar.
Real Madrid ƴan wasa 11: Courtois, Vazquez, Tchouameni, Asencio, Fran Garcia, Ceballos, Valverde, Bellingham, Arda Guler, Mbappe, Vinicius Jr.
Ƴan benci: Lunin, Mestre, Modric, Rodrygo, Endrick, Vallejo, Brahim, Youssef, Jacobo, Munoz.

Asalin hoton, Getty Images











