Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd da Liverpool na son Eze, Pochettino na dab da zama kocin Amurka
Manchester United na sa ido a kan ɗan wasan gaba na gefe na Crystal Palace Eberechi Eze kuma watakila ta nemi ɗan Ingilan mai shekara 26 a bazara mai zuwa. (Manchester Evening News)
Ita ma Liverpool ƙila ta nemi Eze idan Mohamed Salah, bai sabunta zamansa a ƙungiyar ba. (Liverpool Echo)
Chelsea na sa ran sayar da matashin ɗan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana mai shekara 21 ga ƙungiyar AEK Athens ta Girka - kasuwar ƴan wasa ta Girka na ci gaba da ci har zuwa gobe Laraba. (The Athletic)
Ana dab da tabbatar da tsohon kociyan Chelsea da Tottenham Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horad da 'yan wasan tawagar Amurka bayan ganawa da jami'an ƙwallon ƙafa na ƙasar. (Mail)
Manchester United na son ta bayar da aron ɗan wasanta na gaba na gefe Antony na Brazil, kuma Fenerbahce ce kan gaba a masu son ɗan wasan na Brazil. (Sun), external
Galatasaray na son sayen ɗan bayan Tottenham Ben Davies na Wales, kafin a rufe kasuwar ƴan wasa ta Turkiyya a ranar 13 ga watan nan na Satumba. (Takvim, daga Football Insider)
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Chelsea John Obi Mikel ya yi ƙoƙarin ya shawo kan e Victor Osimhen, ya je Blues, kafin tafiyarsa aro daga Napoli zuwa Galatasaray. (Talksport)
Wataƙila tsohon ɗan bayan Real Madrid da Sifaniya Sergio Ramos ya tafi ƙungiyar Corinthians ta Brazil. Ɗan wasan mai shekara 38 ya kasance ba shi da ƙungiya tun da ya bar Sevilla a bazara. (Itatiaia )
Har yanzu Juventus na neman ƙungiyar da za ta sayi ɗan wasanta na tsakiya, Arthur Melo, na Brazil mai shekara 28, wanda yake son ya ci gaba da zama a ƙungiyar. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan gaba na Kanada Jonathan David, na tattaunawa kan sabon kwantiragi da Lille amma kuma ana ci gaba da danganta shi da tafiya gasar Premier. (Teamtalk)
Albashin da ɗan wasan tsakiya Adrien Rabiot, ke nema ya yi wa Manchester United yawa sosai ta ɗauke shi. Ɗan Faransan ba shi da ƙungiya tun da ya bar Juventus. (Football Insider)