Haaland ne gwarzon Etihad na watan Agusta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Erling Haaland shi ne ya lashe ƙyautar gwarzon watan Agusta a Etihad, saboda rawar da ya taka a Premier League.

Ɗan wasan tawagar Norway ya ci ƙwallo bakwai a wasa uku a Premier League a watan na Agusta, wanda ya ci Ipswich da West Ham da kuma Chelsea.

Ya fara da cin Chelsea a wasan makon farko da Manchester City ta yi nasara 2-0 a Stamford Bridge ranar 18 ga watan Agusta.

A wasan mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila, Haaland ya ci Ipswich uku rigis a karawar da City ta yi nasara 4-1 ranar 24 ga watan Agusta a Eihad.

Haka kuma a karawar mako na uku a Premier League Haaland ya kara cin uku rigis a wasan da City ta je ta doke West Ham 3-1 ranar 31 ga watan Agusta.

Kawo yanzu City, tana ta ɗaya a kan teburin Premier da maki tara, iri ɗaya da na Liverpool, wadda itama ta lashe dukkan karawa uku da fara kakar nan.

City za ta karɓi bakuncin Brentford a wasan mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 14 ga watan Satumba.

Daga nan Inter Milan za ta ziyarci Etihad, domin buga wasan farko da City a Champions League ranar Laraba 18 ga watan Satumba.

City na fatan lashe Premier League na biyar a jere, wadda take da tarihin rike da huɗu a jere.