Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na zawarcin Costa don maye gurbin Onana, Arsenal na son Nico Williams
Manchester United ta tura wasu wakilai da za su bibiyi golan Porto da Portugal Diogo Costa mai shekara 25 yayin da suke neman wanda zai maye gurbin mai tsaron ragar Kamaru Andre Onana mai shekara 29. Manchester City ma na zawarcin Costa wanda akwai damar sayar da shi kan fam miliyan 64.3. (Correio da Manha - in Portuguese)
Arsenal ta soma tattaunawa kan ɗauko ɗanwasan Sporting CP da Sweden Viktor Gyokeres mai shekara 26 a farkon kasuwar musayar ƴanwasa ta lokacin bazara. (Football Insider)
Arsenal na ƙyalla ido kan ɗanwasan Athletic Bilbao ɗan asalin Sifaniya Nico Williams mai shekara 22 sai dai ɗanwasan bai gama yanke shawara ba kan ko zai bar kulob ɗin a bazara. (GiveMeSport)
Ɗanwasan Manchester City Nico O'Reilly mai shekara 20, zai ƙulla sabon kwantiragi da ƙungiyar bayan da Chelsea ta bayyana sha'awarta kan ɗanwasan tsakiya na Ingila a matakin ƴan ƙasa da shekara 20. (Fabrizio Romano)
Manchester United ta ci gaba da tattaunawa da wakilin ɗanwasan RB Leipzig da Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 21, tun bayan da ya yi watsi da koma wa Old Trafford a 2022. (Manchester Evening News)
Tottenham Hotspur na duba tayin fam miliyan 30 kan ɗanwasan Chelsea da Portugal Renato Veiga mai shekara 21. (Football Insider)
Manchester United na sa ran samun tayi daga ƙungiyoyin gasar Zakarun Turai kan ɗanwasan ƴan ƙasa da shekara 18 Harry Amass mai shekara 18 a bazara. (GiveMeSport)
Aston Villa na duba yiwuwar cefanar da ɗanwasan Ingila Ollie Watkins mai shekara 29 kan tsakanin fam miliyan 50 zuwa miliyan 60 tare da ɗauko ɗanwasan da ke zaman aro Marcus Rashford mai shekara 27 daga Manchester United a mataki na dindindin. (Football Insider)
Bayer Leverkusen ba za ta hana Xabi Alonso barin kulob ɗin ba idan ya amince ya zama kocin Real Madrid a bazara. (Fabrizio Romano)