Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lewandowski ba zai yi wasan karshe a Copa del Rey da Real ba
Robert Lewandowski ba zai buga wasan karshe a Copa del Rey da Barcelona za ta kara da Real Madrid a cikin Afirilun nan ba.
Dan wasan ya ji rauni ranar Asabar a fafatawar da Barcelona ta doke Celta Vigo 4-3, inda hakan ya sa ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga na bana.
Barcelona ba ta fayyace ranar da zai koma taka leda ba, bayan auna girma raunin da ya ji, sai dai wasu rahotanni na cewar Lewandowski zai yi jinyar mako uku.
Kenan ba zai buga La Liga da Barcelona za ta kara da Mallorca da wasan Copa del Rey da Real Madrid da wasan farko a daf da karshe da Inter a Champions League.
Haka kuma watakila ba zai yi wasan La Liga da Valladolid ba, idan Lewandowski ya warke da wuri ya samu koshin lafiya zai yi wasa na biyu da Inter a gasar zakarun Turai.
Idan kuwa bai samu koshin lafiya da wuri ba, watakila ba zai buga wasa na biyu ba da Real Madrid a La Liga.
Wasannin da ake hasashen Lewandowski ba zai yi wa Barcelona ba:
La Liga ranar Talata 22 ga watan Afirilu
- Barcelona da Mallorca
Copa del Rey ranar Asabar 26 ga watan Afirilu
- Barcelona da Real Madrid
Champions League ranar Laraba 30 ga watan Afirilu
- Barcelona da Inter Milan
Spanish Primera Liga ranar Asabar 3 ga watan Mayu
- Valladolid da Barcelona
Champions League ranar Talata 6 ga watan Mayu
- Inter Milan da Barcelona
La Liga ranar Lahadi 11 ga watan Mayu
- Barcelona da Real Madrid
Lewandowski ya buga wasa na 100 a La Liga a Barcelona ranar Asabar a fafatawar da suka yi a Estadi Olimpic Lluis Companys, wanda yake kaka ta uku a ƙungiyar.
Lewandoeski ya buga wa Barca wasa 48 a kakar nan a La Liga da Champions League da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup da cin ƙwallo 40.
Guda 25 a La Liga da 11 a Champions League da uku a Copa del Rey da kuma ɗaya a Super Cup.
Ƙwallo 25 da ya ci a La Liga, shi ne kan gaba a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar uku tsakani da Kylian Mbappe, wadda yake na biyu a kakar nan.