Mbeumo na son zuwa Man Utd, Barcelona na tattaunawa da Diaz

Bryan Mbeumo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan gaba a Brentford Bryan Mbeumo na son tafiya Manchester United, wanda tuni sun shirya soma tattaunawa da matashin mai shekara 25 dan asalin ƙasar Kamaru. (Athletic - subscription required)

Inter Milan na fatan cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba a Manchester United da Denmark, Rasmus Hojlund mai shekara 22. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Manchester United na kuma jiran ta ji hukuncin da ɗan wasan tsakiya a Portugal Bruno Fernandes ya yanke kan ci gaba da zama da su ko akasin haka, yayin da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ke nuna zawarcinta kan ɗan wasan mai shekara 30. (Sky Sports)

Ɗan wasan gaba a Crystal Palace da Faransa, Jean-Philippe Mateta mai shekara 27, na cikin 'yan wasan da Manchester United ke zawarci amma tana fuskantar kalubale daga Juventus da AC Milan. (Teamtalk)

Myles Lewis-Skelly mai shekara 18 na shirin cimma sabon kwantiragi da Arsenal a wannan kaka, matakin da zai kawo karshen jita-jitar tafiyarsa Real Madrid. (Mail)

Liverpool ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Jamus, Florian Wirtz zuwa 2030, amma har yanzu ba su daidaita kan kudin da ya kamata a biya matashin mai shekara 22 ba, wanda Bayer Leverkusen tayi watsi da yuro miliyan 130 a kansa. (Bild - in German)

Barcelona ta soma tattaunawa da ɗan wasan Liverpool, Luis Diaz mai shekara 28, sai dai yana samun tayi daga Saudiyya. (Florian Plettenberg)

Chelsea na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasa daga Everton, Jarrad Branthwaite mai shekara 22, yayin da Tottenham ke kalubalantarta. (Teamtalk)

Ɗan wasan tsakiya Jobe Bellingham ya zaɓi tafiya tsohuwar ƙungiyar kaninsa, Borussia Dortmund a maimakon Eintracht Frankfurt da RB Leipzig. (Bild - in German)

Chelsea na farautar ɗan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20, Jamie Gittens, wanda ake kiyasata kudinsa kan £50m. (Guardian)

Manchester City na dab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan AC Milan da Netherlands, Tijjani Reijnders mai shekara 26. (Football Italia)

Everton da Manchester United da West Ham na farautar ɗan wasan Serbia, Aleksandar Mitrovic, wanda Al-Hilal ke shirin rabuwa da shi. (Talksport)

Brighton na bibbiyar ɗan wasan Sheffield United, Ollie Arblaster mai shekara 21. (Teamtalk, external)

Tsohon ɗan wasan Arsenal da Ingila, mai shekara 33, Jack Wilshere, na gab da zama koci a ƙungiyar League One ta Plymouth Argyle. (Sun)