Benzema ba zai buga gasar Kofin Duniya ba

Karim Benzema

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Ɗan wasan gaba na Faransa kuma gwarzon ɗan ƙwallon duniya na bana, Karim Benzema, ba zai buga gasar Kofin Duniya da ake shirin farawa ba a yau a Qatar.

Benzema mai shekara 34 ya sake jin rauni a jiya Asabar yayin atasayen da tawagar Faransa ke yi jim kaɗan bayan ya murmure daga raunin da ya ji tun da farko.

"Raina ya ɓaci sosai game da Karim, wanda ya ɗauki gasar nan da muhimmanci sosai," in ji kocin Faransa Didier Deschamps.

Shi kuwa Benzema bayyana alhininsa ya yi. "A rayuwata, ban taɓa sarewa ba amma a yau dole ne na jajanta wa tawagarmu kamar yadda na saba," a cewarsa.

"Dalili shi ne dole ne na bar wa wani gurbina wanda zai taimaki tawagarmu buga wasa mai kyau a Kofin Duniya."

Faransa za ta fara wasanta da Australiya a ranar Talata.

Benzema ya bi sawun ɗan bayan Faransar, Presnel Kimpembe, wanda shi ma ya bar tawagar saboda rauni.

Da ma tawagar ta yi rashin Paul Pogba da Ngolo Kante tun kafin ta je Qatar.

Ita ma tawagar Senegal za ta buga gasar ba tare da tauraron ɗan wasanta ba Sadio Mane.