Mahaya dawaki, masu jimami kan bacewar mutane na cikin hotunan Afirka na wannan mako

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan wata yarinya ce rike da 'ya'yan mangoro a birnin Obour da ke kasar Masar, wanda ya kasance lokacin girbar 'ya'yan itace farawa daga watan Yuni zuwa Nuwamba.
An wallafa
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A can Moroko kuwa a ranar Asabar, wasu mutane ne kan dawaki ke daga makamansu lokacin da ake gasar tseren dawaki ta al'adar Moussem da aka gudanar a birnin Rabat.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An yi ta harba bindigogi a sama yayin bikin na tseren dawaki.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A can wani yanki na kasar Kenya, wata mata ce goye da 'yarta lokacin da take tafiya domin kada kuri'a a zaben 'yan majalisar wakilai da aka jinkirta a mazabar Rongai.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan, wata mata ce ke rawa a jihar Adamawa da ke Najeriya a ranar Talata, lokacin da iyalai wadanda 'yan uwansu suka bace ke bikin ranar bacewar mutane ta duniya.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A nan kuma a ranar Talata, wata mai kayan kawa 'yar kasar Kudancin Sudan, Majda John Peter, lokacin da take takawa a bikin 'yan kayan kawa na duniya na 2022.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ta kasa rike murnar ta bayan lashe gasar, inda ta barke da kuka.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Nan kuwa a ranar Laraba a Sudan, wani mai zanga-zanga na nuna yatsu biyu na alamar zaman lafiya lokacin zanga-zangar nuna adawa da mulkin soji.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wata mata kenan ke nuna goyon bayanta ga wani dan adawa Crepin Mbouli Goumba, da ke adawa da sake fasalta kundin tsarin mulki wanda mutane ke fargabar cewa zai baiwa shugaba Faustin Archange Touadera sake komawa mulki karo na uku.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan kuma, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ke karbar wata kyauta lokacin da ya kai ziyara Algeria a ranar Asabar.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ya kuma kai ziyara cocin Santa Cruz a birnin Oran na kasar ta Algeria.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne Paparoma Francis ya baiwa Bishop Peter Ebere Okpaleke na Najeriya mukamin cardinal a birnin Vatican.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Daga bangaren addini sai kuma wasanni, inda nan wani mai wasan golf dan kasar Afirka ta Kudu, Thriston Lawrence ke buga wasa a ranar Lahadi a Switzerland.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tsohon dan takarar shugaban kasa a Uganda, Bobi Wine ke kamfe dinsa na ganin an sake fursunonin siyasa lokacin da ya halarci bikin nuna fina-finai ta Venice a ranar Alhamis.