Tuchel na tsaka mai wuya a Bayern, Barca za ta sayar da Raphinha

An wallafa

Danwasan tsakiya na Jamus Jamal Musiala, ya yi watsi da sabon tayin da kungiyarsa ta Bayern Munich ta yi ma sa, inda yake son buga gasar Firimiya a bazara yayin da ake alakanta danwasan mai shekara 21 da kungiyoyin Manchester City da Liverpool. (Star)

Watakil a kori manaja Thomas Tuchel idan kungiyar Bayern Munich ta yi rashin nasara Champions League a wasan da za su buga da Lazio ranar Talata mai zuwa. (Sky Sports Germany - in German)

Manajan Manchester United Erik ten Hag, na sanya ido kan mai tsaron gida na Sifaniya Miguel Gutierrez mai shekara 22, kafin a bude kasuwar saye da sayar da 'yanwasa a lokacin bazara. (Sun)

Liverpool na son kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim, sai dai har yanzu ana ganin manajan Bayer Leverkusen Xabi Alonso ne a sahun gaba a wanda ake ganin zai gaji Jurgen Klopp. (Mirror)

Ta yiwu murna za ta koma kan fatan da Barcelona, ke yi na dauko manajan Brighton wato Roberto de Zerbi a lokacin bazara, idan suka gagara daidaitawa kan yuro miliyan 15, kan dan kasar Italiyar kafin ya bar kulub din. (Sport - in Spanish)

Barcelona ta tattauna da tsohon manajan Jamus Hansi Flick, kan maye gurbin Xavi. (Florian Plettenberg)

Dan wasan gaba na Faransa mai taka leda a Paris St-Germain, Kylian Mbappe sun gana da Luis Enrique domin tattauna hargitsin da suka yi tsakanin dan wasan mai shekara 25, da kociyan dan Sifaniya a wasannin da suka yi na baya-bayan nan. (ESPN)

Kungiyoyin Fulham, Everton, West Ham da Wolves na ribibin danwasan tsakiya na Ivory Coast, mai taka leda a Galatasaray Wilfried Zaha mai shekara 31. (Ekrem Konur)

Kungiyoyin Arsenal da Manchester City na son matashin danwasan Fiorentina, kuma na bayan Italiya a ajin 'yan kasa da shekara 21 Michael Kayode. (Fichajes - in Spanish)

Barcelona za ta sayar da danwasan tsakiya na Brazil Raphinha, mai shekara 27, da ɗanwasan baya na Faransa Jules Kounde, mai shekara 25, a lokacin bazara. (Sport - in Spanish)