Chelsea ta tuntubi Man City ko za a sayar mata da Sterling

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta tuntubi Manchester City kan ko za a sayar mata da dan kwallon tawagar Ingila, Raheem Sterling.
Sterling, wanda ya koma Etihad daga Liverpool kan fam miliyan 49 a 2015, ya ci kwallo 131 a wasa 339, yana cikin manyan 'yan kwallon da Chelsea ke son dauka a bana.
An fahimci cewar kawo yanzu Chelsea ba ta taya dan wasan wai shekara 27 ba.
Saura kaka daya yarjejeniyar Sterling ta kare a Etihad, ana kuma tunanin da kyar ne idan zai ci gaba da zama a City.
Sterling, wanda ya buga wa Ingila wasa 77, na son buga wasa a koda yaushe, ba zaman benci ba.
Zai kanacewa na farko da Chelsea za ta dauka tun bayan da aka sayar da kungiyar da Boehly ke jan ragama tun daga watan Mayu.
Chelsea na fatan kara karfin kungiyar a kakar da za a shiga, bayan da ta bayar da aron Romelu Lukaku ga Inter Milan kan yarjejeniyar kaka daya.
Tun bayan da Pep Guardiola ya zama kociyan City a 2016, ba dan wasan da ya ci kwallaye da yawa kamar Sterling mai 120, bayan Sergio Aguero mai 124 a Premier.
Sterling ya zura kwallo 13 a wasa 30 a Premier League da aka karkare, wanda ya lashe kofi na hudu a babbar gasar tamaula ta Ingila, kuma kofi na tara a kaka bakwai a Etihad.









