Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin.
Sai ku tara a shirinmu na gaba - sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke cewa mu wuni lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Mohammed Abdu
Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin.
Sai ku tara a shirinmu na gaba - sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke cewa mu wuni lafiya.
Juventus na fatan kamma cinikin Paul Pogaba ranar Alhamis in ji Sky.
Ana sa ran Pogba zai amince da kunshin yarjejeniyar kaka hudu, wato shekara uku da yarjejeniyar tsawaitata kaka daya.
Club chiefs will meet Pogba's representative Rafaela Pimenta on Thursday and are expected to discuss the
Idan sun cimma matsaya ana sa ran tsohon dan kwallon Manchester United zai je Turin tsakanin 5 zuwa 8 ga watan Yuli domin auna koshin lafiyarsa. ,

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United na auna koshin lafiyar Nick Pope kan batun komawa kungiyar da taka leda daga Burnley kan fam miliyan 10.
Tun farkon makon nan Newcastle United ta amince ta farashin da Burnley ta yi wa dan kwallon.
Pope yana daga cikin 'yan wasan da Newcastle ta dauka da suka hada da Martin Dubravka da Karl Darlow da kuma Mark Gillespie a karkashin Eddie Howe.
Leeds ta yi wa Raphinha kudi a kan fam miliyan 65, inda Tottenham, da Chelsea da Barcelona ke sha'awarsa. (Fabrizio Romano)
Nice na neman kulla yarjejeniyar daukar aron mai tsaron ragar Chelsea, dan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 27. (Foot Mercato)
Chelsea za ta bayar da damar sayar wa West Ham dan wasanta mai kai hari, dan Albania Armando Broja, mai shekara 20, inda ake sa ran za ta taya shi fam miliyan 25. (Express)
Watakila Brighton ta sayo dan wasan tsakiya na Reims da Zimbabwe Marshall Munetsi, mai shekara 26 domin maye gurbin Yves Bissouma, dan wasan tsakiyarta na Mali wanda ya tafi Tottenham. (Mail)

Asalin hoton, Getty Images
Bournemouth ta dauki tsohon dan wasan Fulham da West Ham, mai tsaron baya Ryan Fredericks kan kwantiragin kaka biyu.
Dan kwallon zai koma Bournemouth, bayan da kwantiraginsa ya kare a West Ham a karshen kakar da aka karkare.
Fredericks ya yi kaka biyu a wasannin aro a Craven Cottage.

Asalin hoton, Getty Images
West Brom ta kammala daukarJed Wallace kan yarjejeniyar kaka hudu.
Mai shekara 28 ya koma Millwall, kungiyar da ya ci kwallo 37 goals a gasar Championship.

Asalin hoton, g
Southampton na kokarin hana kungiyoyin Manchester City da Manchester United da Tottenham da West Ham zawarcin dan wasanta na tsakiya, dan Ingila James Ward-Prowse mai shekara 27, inda ta yi masa farashin fam miliyan 75. (Give Me Sport)
Babban jami'in Bayern Munich Oliver Kahn ya ce yana sa ran Robert Lewandowski, ya ci gaba da zama a tare da zakarun na Jamus a bazaran nan. (Sky Sports)
Manchester City ta yi nisa a tattaunawar da take yi ta cinikin dan bayan Brighton da Sifaniya Marc Cucurella. (Football Insider)
Leeds United na duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na gefe na PSV Eindhoven da Holland Cody Gakpo, a bazaran nan a matsayin wanda zai maye gurbin Raphinha,na Brazil, wanda Arsenal ke so. (Foot Mercato)

Asalin hoton, Getty Images
Christopher Nkunku, wanda aka yi ta danganta shi da komawa both Manchester United ko Chelsea, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a RB Leipzig zuwa karshen kakar 2026.
Dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 24, ya ci kwallo 20 league ya kuma bayar da 13 aka zura a raga a karawa 34 a lik a 2021-22, ya kuma dauki German Cup a watan Mayu.
.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Najeriya ta yi amai ta lashe kan batun yanyewa daga shiga wasannin kwallon kwando a duniya kaka biyu.
Ministan wasannin kasar ne ya sanar cewar sun dauki hukuncin ne bayan takaddamar shugabancin hukumar kwallon kwando ta Najeriya.
Najeriya za ta koma buga wasannin, bayan taro da aka gudanar tsakanin shugabannin kwallon kwando na duniya da ministan wasa Sunday Dare.
Wata wasika daga Fiba ta amince da Musa Kida a matakin shugaban hukumar kwallon kwando ta Najeriya.
Hakan na nufin Najeriya za ta ci gaba da buga wasannin neman shiga kofin duniya da za a yi a Rwanda a wata mai zuwa, inda za ta fafata da Mali da Uganda da kuma Cape Verde.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Bisa ga dukkan alamu golan Liverpool dan Jamus Loris Karius, mai shekara 29, na shirin jarraba sa'arsa a wata kungiyar, kasancewar ba makawa zai bar Anfield. (Sky Germany)
Shi kuwa dan wasan gaba na Real Madrid da Sifaniya Marco Asensio, mai shekara 26, ya fi kaunar tafiya Liverpool ne maimakon AC Milan. (Mail)
Chelsea na jiran tafiyar Romelu Lukaku, aro Inter Milan ta kammala kafin, kungiyar ta tunkari maganar sayen dan gaban Manchester City da Ingila Raheem Sterling. (Sky Sports)
Matashin dan wasan Brazil Vinicius Jr, mai shekara 21, ya ce, zai ci gaba da zama a Real Madrid duk da sha'awarsa da Paris Saint-Germain ke yi. (Mail)

Asalin hoton, Getty Images
Idan anjima da yamma za a raba jadawalin zagayen farko a Caraboa Cup da kungiyoyi 70 za su fafata masu buga buga Championship da League One da kuma League Two.
Kungiyoyin da ke buga Premier League su 13 da ba sa buga gasar zakarun Turai za su fara daga zagaye na biyu.
Za a buga wasan karshe a Caraboa Cup na 2023 a Wembley ranar Lahadi 26 ga watan Fabrairu.
Liverpool ce ke rike da kofi.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Nottingham Forest na daf da daukar Taiwo Awoniyi daga Union Berling mai buga gasar Bundesliga.
Awoniyi da mai kula da wasanninsa na tattaunawa kan komawa buga Premier League kan fam miliyan 17.7, bayan da Forest ke son biyan kunshin kwantiraginsa.
A wasa 31 da ya buga a Bundesliga a kakar da ta kare, tsohon dan kwallon Liverpool ya zura 15 a raga a kungiyar da ta yi ta biyar a Bundesliga.

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tawagar Denmark, Mikkel Damsgaard yana daga cikin wadanda suka haskaka a Euro 2020, ana mamakin yadda ya ci gaba da taka leda a Sampdoria, bayan rawar da ya taka.
Daga nan dan kwallon ya yi jinyar da ta hana shi buga kakar Serie A da aka kammala, daga baya ya murmure har ya samu damar buga wa Denmark wasannin Nations League.
Tuni ake rade-radin cewar kungiyoyin Premier League na son daukar Damsgaard a bana.
Sai dai kuma da alamu dan wasan zai ci gaba da taka leda a Sampdoria har zuwa bayan gasar kofin duniya.

Asalin hoton, Reuters
Dan wasan gaba na Ajax dan Brazil Antony, mai shekara 22, ya kuduri aniyar tafiya Manchester United a bazaran nan. (Goal)
Kociyan Barcelona Xavi na rokon Ousmane Dembele, ya yarda ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar, yayin da Chelsea ke nuna saha'awarta a kan dan wasan na Faransa. (Goal)
Mai yuwuwa a sayar da dan wasan baya na Manchester United da Ingila Brandon Williams, mai shekara 21, a kan fam miliyan 10. (Sun)
Ajax za ta kara taya dan wasan gaba na gefe na Tottenham Hotspur dan Holland Steven Bergwijn, mai shekara 24, amma kuma kungiyar ta Premier ba za ta karbi kudin da yake kasa da fam miliyan 25 ba. (Sky Sports)

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran Manchester United za ta sake taya dan kwallon Barcelona, Frenkie de Jong, in ji Manchester Evening News.
Tun farko United ta taya dan wasan kan fam miliyan 51.64 har da karin tsarabe-tsarabe, amma Barcelona taki sallama tayin.
Wasu rahotanni na cewar kungiyar Camp Nou na bukatar fam miliyan 64.55.

Asalin hoton, Getty Images
Juma'a, 29 ga watan Yuli
Huddersfield da Burnley
Asabar, 30 ga watan Yuli
Blackburn Rovers da QPR
Blackpool da Reading
Cardiff City da Norwich City
Hull da Birstol City
Luton da Birmingham
Millwall da Stoke
Rotherham da Swansea
Wigan da Preston
Middlesbrough da West Brom
Lahadi, 31 ga watan Yuli
Sunderland da Coventry
Litinin, 1 ga watan Agusta
Watford da Sheffield United
Ma'aikatan lafiya takwas za su gurfana gaban kotu da laifin sakaci kan mutuwar tsohon dan kwallon duniya Diego Maradona.
Maradona ya mutu a watan Nuwamban 2020 a gidansa dake Buenos Aires, sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60.
Kafin mutuwarsa ya yi jinya bayan an yi masa tiyata a farkon watan da ya rasu.
Sai dai yan kwanaki bayan mutuwarsa ne masu shigar da kara suka kaddamar da binciken likitoci da sauran ma'aikatan lafiyar da suka yi jinyarsa.
Kuma a bara ne suka bada rahoton cewa akwai sakaci da rashin kwarewa ga wasu daga cikin ma'aikatan lafiyar da suka yi jinyar tasa.
Idan aka kama su da laifi a mutuwar tsohon dan kwallon na Argentina, za su iya fuskantar daurin shekaru 25 a gidan yari, kamar yadda kundin sharia a kasar ya tana da.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3